Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 17:02:33    
Baki na sha'awar koyon Sinanci

cri

Tare da saurin cigaban tattalin arzikin kasar Sin da Karin mu'amala da take yi da kasashen waje,matsayin Sinanci ya kara daguwa a duniya.Dayake ana ganin cewa Sinanci na daya daga cikin harsunan duniya masu wuyan koyo,mutanen dake koyon Sinanci sai kara yawa suke a duniya cikin shekarun baya.

Kerstin Storm wata daliba ce a jami'ar Minstel ta Jamus,tun lokacin da take babbar makarantar middle tana sha'awar harshen Sinanci da kasar Sin. Bayan da ta shiga jami'a sai ta fara koyon Sinanci.A lokacin nan iyalinta da aminanta ba su goyi bayanta koyi Sinanci ba.A ganinsu Sinanci na da wuyan koyo,kasar Sin kuma na nesa da Jamus,duk da haka Kerstin ta daura niyyar koyon Sinanci.

Bayan da ta shafe shekaru hudu wajen nazarin Sinanci,ga shi yanzu ta iya magana da Sinanci.Ta gaya wa wakilinmu cewa koyon harshen Sinanci wani zabi ne mai kyau."A kasar Jamus babu mutane da yawa dake magana da Sinanci,a ganina koyon Sinanci na da amfani gare ni wajen samun aikin yi.Ga shi a yanzu da akwai dama da yawa a kasar Sin,kamfanonin Jamus da dama sun kafa rassansu a kasar Sin,dangantakar kasuwanci dake tsakanin Jamus da kasar Sin sai kara karfi take."

Kerstin za ta kammala karatunta a jami'a a shekara mai zuwa.Tana so ta zama 'yar jarida.Shekara daya ke nan da ta zo nan birnin Beijing cikin lokacin hutu,ta yi aiki a ofishin wata jaridar Jamus a nan birnin Beijing.Ta ce idan ba za ta samu aikin dan jarida ba,za ta nemi wani aikin da ya shafi kasar Sin,kamar tana cigaba da zama a jami'a tana koyon tsohon Sinanci da nazarin al'adun kasar Sin.

Kerstin Storm ta ce a halin yanzu a kasar Jamus mutanen dake koyon Sinanci sai kara yawa suke.Lokacin da ta fara koyon Sinanci a aji daya akwai dalibai goma kawai,amma yanzu a aji daya da akwai dalibai 40 dake koyon harshen Sinanci.

A ganin Kerstin,koyon Sinanci yana da ban sha'awa.Tana so ta gaya wa abokanta na Jamus da wadanda suke shirin koyon Sinanci ta gidan rediyonmu cewa yin mu'amala da Sinawa in ka samu dama,kyakkyawar hanya ce da za ka iya kara kwarewarka wajen harshen Sinanci.Ta ce "Idan kana koyon Sinanci,kada ka ji tsoro,za ka iya gane Sinanci ba wuya;Da ka yi magana da Sinawa,in ka gane ya fahimci abin da kake fada,sai ka yi tadi da shi,ta haka za ka iya gane Sinanci ba wuya,za ka kuma kara samun cigaba."

Kamar yadda Kerstin Storm take,wani dalibi mai shekaru 22 da haihuwa da ake kiransa Ahmed na kasar Massar yana sha'awar Sinanci tun lokacin da yake karami.ya ga hajojji iri iri da iyalinsa ya saye daga kasuwanni,a jikin hajojji da akwai alamun "made in China",daga nan ya fara sha'awar kasar Sin da kaunarta.Da ya shiga jami'a,ya fara koyon Sinanci.Bayan shekaru uku na karatu,Mista Ahmed ya iya magana da Sinanci.Ya ce"Sinanci ya zama harshe na biyu gare ni.Ina sha'awar Sinanci sosai,abin alfahari ne gare ni da na iya karanta jaridu da mujalloli da littattafan dake dauke da kagaggun labarai na Sinanci."

Tare da cigaban tattalin arzikin kasar Sin,kasar Sin ta kara mu'amala da kasashen ketare.Mutanen dake koyon harshen Sinanci a dundiya sun rika karuwa.suna zama a Asiya da Turai da Amurka da kuma Afrika.Masu koyon Sinanci ba daliban dake koyon harshe da al'adu da tarihi kawai ba,daliban kasashe da dama dake koyon ilmin tattalin arziki da ciniki da kuma shari'a su ma sun fara koyon Sinanci,A ganinsu iya magana da Sinnanci ya taimaka masu samun aikin yi da aikinsu a nan gaba.