Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-30 20:37:13    
Bunkasuwar kasar Tunisia lami lafiya a cikin shekaru 20 da suka wuce

cri

Yanzu an shiga karshen lokacin kaka ne, ruwan sama ya tsabtace biranen kasar Tunisia sun yi kyau sosai. A kan manyan tituna da gine-gine da ke babban birnin kasar, an sa tutar kasar Tunisia mai launin ja da sauran take daban dabam, kuma ana jin murnar biki ko ina.

Ashe, ranar 7 ga watan Nuwamba ranar cika shekaru 20 da Mr. Ben Ali shugaban kasar Tunisia ya yi rantsuwar kama aikinsa kuma ya bayyana manufar yin gyare-gyare, an yi biki a babban birnin, dubban mutane sun halarci bikin, kuma shugaba Ben Ali ya yi wani muhimmin jawabi, inda ya waiwayi manyan nasarorin da kasar Tunisia ta samu a fannoni dabam daban a cikin shekaru 20 da suka wuce, a sa'I daya kuma, ya yi bayani kan kyakkyawar makomar kasar Tunisia. Jawabinsa ya sami karbuwa daga mutanen da suka halarci biki sosai.

 

A cikin shekaru 20 da suka wuce, kullum Mr. Ben Ali ya tafiyar da manyan manufofin kasa, wato "zaman karko ya sa kaimi ga bunkasuwa, tare da bunkasuwa ta sa kaimi ga zaman karko", kuma ya yi gyare-gyare a jere kan fannonin siyasa, da tattalin arzik. Da farko, game da harkokin siyasa, ya gyara tasrin mulkin kasa, ya tafiyar da tsarin jamhuriyya na majalisar dimokuradiyya na jami'iyyu dabam daban, domin neman raya wata kasa mai zaman jituwa ta hanyoyin yin shawarwari, da kuma a girmamawa hakkin dan 'Adam, da yanci, da adalci da kuma darajar gaskiya. Na biyu, wajen tattalin arziki, Mr. Ben Ali ya kyautata tsarin tattalin arziki, kuma ya canja tsarin tsararren tattalin arziki zuwa tsarin tattalin arziki na kasuwanni. Saboda manufofin da ya tafiya suna da kyau, saurin bunkasuwar jama'ar kasar Tunisia ya yi ta karuwa. yawan kudin kasar Botswana ya samu daga wajen samar da kayayyaki ya karu daga dolar Amurka biliyan 5.77 a shekarar 1986 zuwa dolar Amurka biliyan 35.69 a shekarar 2007, kuma matsakaicin yawan kudin da ko wane mutumin kasar Tunisia ya samu ya kai dolar Amurka 3463.4, wannan ya karu da ninka sau hudu bisa na shekarar 1987.

Kullum kasar Tunisia tana mai da hankalinta sosai wajen bautawa jama'a, gwamnatin kasar ta kashe kashi 56.2 cikin kashi 100 na kasafin kudi kan fannonin manyan gine-gine, da aikin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da gidajen kwana, da ciyar da tsofaffin mutane. Wata mace mai aikin shara ta ce, yaranta biyu suna makarantar firamare, idan sun sami maki yadda ya kamata, za su shiga jami'a ba tare da biya kudin karatu ba, saboda haka, yawan yara da suka shiga makaranta ya kai kashi 99 cikin kashi 100.

 

Ban da haka kuma, gwamnatin kasar ta kafa "asusun gidajen kwana" domin ba da iyakacin taimako ga matasa da su warware matsalar gidajen kwana. Wani matasa wanda ke aikin a hukumar watsa labaru ta kasar Tunisia ya ce, ya sami bashi bisa saukakan sharudda ta "asusun gidajen kwana", zai iya biyan duk bashi a cikin shekaru 15 zuwa 20 masu zuwa. Bisa kididdigar da aka yi, saboda wannan tsari na "asusun gidajen kwana", kashi 80 cikin kashi 100 na iyalin kasar Tunisia suna da gidajen kwana na kansu.

Wajen kiwon lafiya, gwamnatin kasar Tunisia ta yi kokari sosai. A kasar Tunisia, bayan wani mutum ya biya kudin rajista kadan, zai iya samun magani ba tare da biyan sauran kudi ba. Saboda an inganta zaman jama'ar kasar Tunisia sosai, kuma an warware matsalolin ba da limi, da gidajen kwana, da kiwon lafiya, matsakaicin tsawon rayuwar jama'ar kasar ya kai shekaru 74 da haihuwa, kuma mai yiyuwa ne zai kai shekaru 80 a shekarar 2020.