Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-30 15:39:06    
Gasar kacici-kacici dangane da cikon shekaru 45 da kafauwar sashen Hausa

cri
A ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 1963 ne aka kafa sashen Hausa na rediyon kasar Sin, wato yanzu shekaru kusan 45 ke nan muna watsa muku shirye-shirye da muryar Hausa, kuma ranar 1 ga watan Yuni na shekara mai kamawa za ta kasance ranar cika shekaru 45 da kafuwar sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Domin taya murnar wannan muhimmiyar rana, tun daga ranar 1 ga watan Disamba na wannan shekara har zuwa karshen watan Afrilu na shekara mai zuwa, za mu gudanar da wata gasar kacici-kacici dangane da tarihin sashen Hausa, amma masu sauraro, abin lura shi ne, a maimakon mu turo muku tambayoyi kamar yadda muka saba yi a da, a wannan karo, muna so ku yi kokarin rubuto mana bayani da ke da taken "Ni da Sashen Hausa na CRI", wato ku fada mana ra'ayoyinku a kan sashen Hausa ko kuma irin labaran da suka faru a tsakaninku da sashen Hausa. Za mu gabatar da kyawawan bayananku a kai a kai a filinmu na "amsoshin wasikunku", kuma bayan da muka kawo karshen gasar, za mu fitar da wadanda suka fi kwarewa, don mu ba su kyaututtuka kamar yadda muka saba yi a da. Masu sauraro, muna muku marhabin da shiga gasar cikin himma. Kada kuma ku manta, za mu kawo karshen gasar a karshen watan Afrilu na shekara mai zuwa, kuma kuna iya turo mana bayananku zuwa akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato China Radio International P.O.Box 72100, Victoria Island, Lagos Nijeriya. ko kuma ku aiko mana wasiku zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email kai tsaye a kan Hausa @cri.com.cn.

To, mun dai sanar da ku a kan gasarmu ta kacici-kacici dangane da tarihin sashen Hausa. A hakika dai, mun sha samun tambayoyin masu sauraro a kan tarihin sashen Hausa, kuma domin kara fadakar da masu sauraronmu a kan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, to, yanzu bari mu dan bayyana muku tarihinsa.

An fara shirin kafa sashen Hausa a nan gidan rediyon kasar Sin ne a karshen shekara ta 1960. A watan Janairu na shekara ta 1961, sashen Hausa ya gayyato wani masanin harshen Hausa daga kasar Nijer don ya koya wa wasu daliban kasar Sin Hausa. Bayan da masanin ya koma gida kuma, an sake gayyato wani masanin harshen Hausa mai suna Amada daga Nijer, wanda kuma shahararren mai watsa labaru ne na gidan rediyon birnin Yamai. Bisa taimakonsa, ma'aikatan kasar Sin sun fara iya Hausa sannu a hankali. A karshen shekara ta 1962, sashen Hausa ya fara watsa labaru. Bisa kokarin da aka shafe watanni da dama ana yi, daga karshe dai, a ran 1 ga watan Yuni na shekara ta 1963, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ya fara watsa labarunsa a hukunce.

A halin yanzu dai, akwai ma'aikatan kasar Sin 15 a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, wato su ne shugaban sashen Hausa Sanusi, da Halima da Umaru da Ali da Halilu da Sani da Jamila da Bilkisu da Lubabatu da Kande da Tasallah da Danladi da Musa da kuma Bello. Bayan haka, muna da masanan harshen Hausa guda uku wadanda suka zo daga kasar Nijeriya, wato Balarabe Shehu Ilelah da Lawal Mamuda da kuma Dr.Salisu Yakasai. A shekara ta 1995, sashen Hausa ya kuma kafa ofishinsa a birnin Lagos na kasar Nijeriya, kuma yanzu wakilinmu Bello yana aiki a ofishin.

A kowace rana, sashen Hausa na rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shiryensa har sau 11 zuwa yankunan Hausa na yammacin Afirka. Wato shirinmu na farko wanda ke zuwa muku daga karfe 5 da rabi zuwa 6 da rabi na yamma, agogon wurin, wanda kuma mu kan maimaita shi daga karfe 6 da rabi zuwa karfe 7 da rabi na yamma. Sa'an nan kuma, mu kan watsa muku shirinmu na biyu daga karfe 7 zuwa karfe 7 da rabi, agogon wurin, da kuma shirinmu na uku daga karfe 9 zuwa karfe 10 na safe. Bayan haka, a birnin Yamai, babban birnin kasar Nijer, muna kuma watsa shirye-shiryenmu har na tsawon awa 7 a kan FM106 da kuma FM104.5. A ko wace rana, sashen Hausa na rediyon kasar Sin yana kawo wa masu sauraronsa muhimman labaru da dumi-duminsu na kasar Sin da na Afirka da kuma na sauran kasashen duniya baki daya. Ban da labarai, sashen Hausa yana kuma gabatar wa masu sauraronsa da shirye-shirye masu kayatarwa, kamar su "mu leka kasar Sin" da "Afirka a yau" da "duniya ina labari" da "al'adun kasar Sin" da "kananan kabilun kasar Sin" da "wasannin Olympics na Beijing" da "Sin da Afirka" da 'musulunci a kasar Sin' da 'zabi sonka' da 'koyon Sinanci' da "yawon shakatawa a kasar Sin" da dai sauransu, wadannan shirye-shirye sun sami karbuwa sosai a tsakanin masu sauraro sabo da ilmantarwa da sakin jiki da kuma mu'amala.

Bisa cigaban fasahar internet, sashen Hausa ya kafa tasharsa ta internet a shekara ta 2003, wato hausa.cri.cn, inda idan masu sauraro suka kama, to, za su iya karanta labarai da dumi-duminsu, kuma suna iya sauraron sabbin shirye-shiryen sashen Hausa a ko da yaushe.

Bunkasuwar sashen Hausa ba ya iya rabuwa da goyon baya da masu sauraronmu suka ba mu, a ko wace shekara, muna samun wasiku masu dimbin yawa daga masu sauraro. A sabo da haka kuma, mun kulla zumunta da aminan Afirka masu yawa, a sa'i daya kuma, ra'ayoyi da shawarwari da aminanmu na Afirka suka ba mu a cikin wasikunsu ma sun taimaka kwarai wajen kara kyautata shirye-shiryenmu. Sabo da haka, dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin muna yi wa masu sauraronmu godiya, kuma muna fatan za ku ci gaba da rubuto mana wasiku ko Email, don taimaka mana a wajen kara kyautata shirye-shiryenmu. (Lubabatu)