Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-30 15:36:17    
Gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya da CRI ta gudanar a game da taron wasannin Olympics na Beijing (babi na biyu)

cri
Aminai masu sauraro, a makon jiya dai, mun karanta muku bayanin musamman na farko da ke da lakabi haka: " Ana gudanar da ayyukan share fagen gasar wasannin Olympics na Beijing lami-lafiya". Yau, za mu ba ku bayanin musamman na biyu a game da gasar wasannin. Sunan bayanin shi ne: " Babban take da kuma abun kawo wa mutane sa'a na gasar wasannin Olympics na Beijing ".

Kamar yadda kuke sanin cewa, za a gudanar da wannan gagarumar gasa a ran 8 ga watan Agusta na shekara mai kamawa. Domin kara yayata hasashen gudanar da gasar wasannin Olympics na Beijing da kuma gwada zurfaffen al'adun kasar Sin ga dukkan kasashen duniya, tuni a shekarar 2005 kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kaddamar da babban take da kuma abun kawo wa mutane sa'a na gasar wasannin daya bayan daya. To mene ne babban taken kuma mene ne abun kawo wa mutane sa'a? ' Babban taken gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 shi ne: Duniya daya kuma buri daya, wato One World One Dream.'

Idan dai ba a manta ba, a ran 26 ga watan Yuni da dare na shekarar 2005, babban jami'in Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Li Changchun ya yi shelar babban taken gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. To, ina ma'anar babban taken? Kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Beijing ta bada amsa cewa, babban taken nan ta bayyana halin zuciya iri daya na dukkan kasashen duniya na samun kyakkyawar makoma ta bil adama duk bisa kwarin gwiwa daga suka manufofin wasannin Olympics; Haka kuma ya bayyana kyakkyawan burin mazauna birnin Beijing da na jama'ar kasar Sin na more kyakkyawar mahaifa da sakamakon wayin kai da kuma kirkiro makoma tare da jama'ar kasashe daban-daban na duniya kafada da kafada.

Mr. Zhang Yiwu, kwararre a fannin wasannin Olympics daga Jami'ar Beijing ya bayyana ra'ayinsa cewa: " Akwai muhimman abubuwa guda biyu dake cikin wannan babban take, wato ke nan duniya da buri. Kalmar ' duniya daya' na nufin cewa kasar Sin tana kishin bude kofa ga kasashen waje domin yin cudanya tare da su; Kuma kalmar ' Buri daya' na nufin cewa kasar Sin da kuma sauran kasashen duniya suna begen gasar wasannin Olympics da zaman lafiya da kuma duk wadanda suka cancanci a girmama su".

Jama'a masu sauraro, daidai a lokacin da babban taken gasar wasannin Olympics ta Beijing ya shiga cikin zukatan jama'a a kwana a tashi kuma a ran 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2005 wato ranar cika kwanaki dubu daya ke nan da suka rage a gudanar da bikin bude wannan gagarumar gasar wasannin, aka kaddamar da kayan dake kawo sa'a na gasar wasannin, wato " Fuwa" guda biyar masu ban sha'awa. Sunayensu su ne:Beibei, Jingjing, Huanhuan, Yingying da kuma Nini da aka kira su bisa lafazin Sinanci. Gaba daya ma'anarsu ita ce: Beijing na yin lale marhabin da kai. Wani babbn jami'in kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya yi babban yabo ga wadannan kananan kayayyakin kawo sa'a, cewa: " Kayan dake kawo sa'a na kunshe da abin da ya kira ' Fuwa' guda biyar, wadanda suke haduwa gu daya kamar yadda yatsu biyar suke. Hakan ya haskaka zobba biyar na Olympics da kuma bayyana yadda bil adama ke yin zama cikin jituwa tare da halitta".

To, madalla jama'a masu sauraronmu, kun dai saurari bayanin musamman na biyu game da gasar wasannin Olympics ta Beijing. A mako mai zuwa, za mu watsa muku bayanin musamman na uku dake da lakabi haka: " Bayani kan fllaye da dakunan wasa na gasar wasannin Olympics ta Beijing". To, sai mako mai zuwa, ku huta lafiya. ( Sani Wang )