----Kare ya sha wahala:Da akwai wani mutum da ake kira shi Zhao a birnin Zhuzhou na lardin Hunan na kasar Sin.Mutumin nan yana da wani babban kare.Wata rana ya zagaya da karensa cikin birnin,yana jin yunwam,sai ya daure karen kan wani katon itace wanda yake da shekar rina a bisa,shi mutumin nan bai sani ba ya tafi abinsa ya je dakin cin abinci. Bayan ya cin abinci, ya koma inda ya daure karen, ashe ya ga rina masu dimbin yawa sun kai hari kan karensa,nan da nan sai ya buga waya zuwa ga 'yan sanda domin neman taimako.Da isowar 'yan sanda,sai sun kore rina da ruwan fesa.an ceto karensa. Duk da haka,karen ya ji rauni mai tsananni.
---Wani dalibi ya rera wakoki domin neman taimako.An sami wani dalibi da ya yi shakatawa wurin Songshan mai shakatawa na gundumar Dengfeng na lardin Henan na kasar Sin.Ya yi wauta ya fadi daga kan wani tsauni mai tsayin mita metan.Da ya fadi kan kasa a wani kwari ba wanda ya gan shi ba,sai dalibin nan ya yi ta rera wakoki cikin sa''o'i sha uku. Masu hawa tsauni sun ji muryarsa sai sun buga wayar salula ga hukumar masu kashe wuta ta hukumar tsaro ta gundumar Dengfeng,daga baya an tura masu ba da taimako aka ja da shi da igiya.
---An samu wani gwarzo a lardin Hunan na kasar Sin.Gwarzon nan sunansa Chen Changsha.Wata rana ya yi doguwar tafiya da dansa, yayin da ya ke cikin jirgin ruwa a kogin,sai jirgin da yake dauke shi da dansa ya ci karo da wani jirgin ruwan daban,nan take jiragen ruwan biyu sun nutse,sai wannan mutum Chen Changsha ya fidar tsoron mutuwa da nuna rashin son kai ya ceci sauran mutanen dake cikin jirgin,bayan da kammala ceton saura,sai ya nemi dansa,ya yi makara,ruwan kogin ya tafi da dansa.Labarinsa ya game ko ina a yankin da ya ke zauane.Halinsa na rashin son kai ya kuma girgiza zukatan mutane.
----An sami wani mutum mai ban mamaki a lardin Jiangsu na kasar Sin.Wani likita ya ce an sami wani mutum mai ban mamaki,wanda ba ya yi barci kamar sauran mutane ba,ko wace rana da dare ya yi barci awa biyu kawai,kuma ya sha ruwa kadan cikin wata daya tun yana da shekaru 18 da haihuwa.Mutumin nan yana da shekaru 61 da haihuwa yana zama a birnin Yangzhou na lardin Jiangsu.ya kan shiga barci a tsakar dare,sai ya tashi da karfe biyu na safe.Halinsa ya dace da aikin dare,shi ya sa an dauke shi a matsayin mai gadi a dare.Bayan da aka yi masa bincike a asibiti,likita ya ce yana da koshi lafiya,kome na tafiya daidai.
---Wata agwagwa ta zamai mai gadi.Wani mutumin da ya yi kiwon tumani ya ya yi horon agwagwa da ta zama mai gadi ga tumakinsa a yankin Jiaozhou na lardin Shandong na kasar Sin.Ko wace rana da safe,agwagwa ta tashi ta ja gaban garukka biyu na tumaki da su ci abinci a filin ciyawa,idan wani bako ya kusanci garukkan,sai agwagwa ta ta da fukafukinta,ta kuma mika wuya,ta kuma yi kuka. An ce tumani na zama tre cikin lumana da agwagwan.Da suka koma gida,agwagwan ta gadi gidan mai gida a dare maimakon tumaki.A cikin shekaru takwas da suka gabata,mai gida bai rasa ko tumaki ko guda ba kuma babu mai sata ya shiga gidansa.
----Wani mutum ya tsira bayan jirgin ruwan ya nutse.Kaftin jirgin ruwan teku ya tsira bayan awoyi 18 da jirgin ruwan da yake aiki a cikin ya nutse.Masu ba da agaji sun isa wurin teku inda jirgin ya nutse suka cece shi.Sunan kaftin nan shi ne Liu Wuchang,mutumin na lardin Taiwan na kasar Sin.Kafin jirginsa ya nutse,ya buga wayar salula.Da aka tura ma'aikata masu ceto da jiragen helicopters zuwa inda jirgin ya nutse ba su ga kome sai tarkacen jirgin kawai.Da jirgin ruwan ya nutse,kaftin ya kama wani guntun katako,ya yi bambaro kan ruwan teku mai nisa kilomita arba'in daga baya aka cece shi.
---- Wani yaro ya yi doguwar tafiya.An sami wani yaro mai shekaru 11 da haihuwa a lardin Taiwan na kasar Sin.Yaron ya yi tafiya ba tare da sanin iyayensa ba.Yaron ya yi tafiya mai tsawon kilomita dari uku cikin yini biyu.Ya je wuraren shan iska a gundumomin Yunlin da Zhanghua da kuma Danshui da Taipei.Ya yi tafiya ne da keken hawa da jirgin kasa da motar bus dake yin tafiya mai nisa.Da 'yan sanda sun iske yaron yana barci a tashar jirginsa kasa.Da aka tambaye shi yadda ya yi tafiya ya ce da kudinsa ya kare a cikin tafiya ya kan sami taimako daga matafiya.Lalle yaron nan yaron ne da ya fi kankanta cikin tafiya mai yanci.
----Wani tangararen yaro ya sha wahala.An sami wani yaro mai shekaru 15 da haihuwa a birnin Jinan na lardin Shandong na kasar Sin.yaron nan ya saba yin barcin dare tare da kulawar mamarsa.Da ya shiga makarantar middle school,sai tilas ya yi barci a dakunan makarantar.sabo da haka ya kasa shiga barci saboda mamarsa ba ta wurinta.daga baya yana so ya bar makaranta.
----An kafa wani gidan Jurassic a jihar Xinjiang na kabilar Ughur mai ikon tafiyar da harkokin kanta.An kfa wannan gidan Jurassic ne a gundumar Jimu Sa'er dake a jihar.An kashe kudin Sin da ya kai kudin Sin RMB miliyan goma wajen gina gidan.Fadin wurin da gidan ke zaune ya kai muraba'in mita 31900.A cikin gidan an nuna dabbobi da kayayyaki na jabu na zamanin can can da wato zamanin Jurassic duk domin fadakar da jama'a kan zamanin tarihi na can can da.
|