Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 16:30:27    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(22/11-28/11)

cri
Ran 21 ga wata, a nan Beijing, madam Tang Xiaoquan, mataimakiyar shugaban gudanarwa ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayyana cewa, ana share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing a fannoni daban daban yadda ya kamata. Ta kuma yi karin bayani cewa, hadaddiyar kungiyar wasan Olympic ta nakasassu ta kasa da kasa ta riga ta tabbatar da ajandar shirye-shirye ta ko wace rana a cikin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Game da gina filayen wasa kuwa, an tabbatar da filaye da dakunan wasa guda 20 domin shirye-shirye da kuma wasu 28 wadanda za a yi amfani da su domin aikin horo, da kuma kauyen 'yan wasa nakasassu da sauran filayen wasa ba domin gasa ba. Ana gina filaye da dakunan wasa yadda ya kamata, haka kuma, ba a gamu da matsala ko kadan wajen kafa kungiyoyin kula da filayen wasa ba. Ban da wannan kuma, an samar da na'urori ba tare da shinge ba a cikin dukkan filaye da dakunan wasa bisa tsattsauran ma'auni. Sa'an nan kuma, ana gudanar da ayyukan karbar baki da daukar masu aikin sa kai domin gasar wasanin Olympic ta nakasassu ta Beijing yadda ya kamata.

Ran 23 ga wata, an kaddamar da tsarin bai wa 'yan kallo bayanai kan wurare a tashar yanar gizo wato Internet da aka bude dangane da gasar wasannin Olympic ta Beijing. Masu yin amfani da wannan tsari za su sami bayanai iri-iri 52 game da wuraren da filaye da dakunan wasa na gasar wasannin Olympic ta Beijing da kantunan sayar da kayayyakin gasar wasannin Olympic ta Beijing bisa iznin musamman da kuma wuraren yawon shakatawa suke da kuma abubuwan da ke shafar al'adu da ko-ta-kwana.

Ran 25 ga wata, a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, an yi bikin jefa kuri'a cikin kungiya-kungiya domin gasar tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2010 da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA ta za ta shirya. A karshe dai, kungiyar kasar Sin ta shiga rukuni na A na yankin Asiya, za ta kara da kungiyoyin kasashen Australia da Iraq da Qatar. A idon mutane, wadannan kungiyoyi 4 na rukuni na A sun fi samun kunnen doki, za su kuma fi gamuwa da gasanni masu tsanani a tsakaninsu, in an kwatanta da sauran rukunoni 4 na yankin Asiya.

Ran 25 ga wata, bisa agogon wurin, a kasar Monaco, hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa wato IAAF ta sanar da cewa, shahararren dan wasan gajeren gudu Tyson Gay na kasar Amurka da kuma 'yar wasan gudu na dogon zango madam Meseret Dafer ta kasar Habasha sun zama 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle maza da mata mafiya nagarta a duniya a shekarar 2007. A cikin gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa da aka yi a birnin Osaka na kasar Japan a watan Agusta na wannan shekara, Gay ya kwashe lambobin zinariya 3 cikin gasannin gudu masu tsawon mita 100 da 200 da kuma na ba da sanda a tsakanin 'yan wasa 4 mai tsawon mita 100. madam Defar kuwa, ta rage matsayin bajimta na duniya na wasan gudu mai tsawon mita dubu 5 da ta rike da shi da dakikoki 8 ko fiye a watan Yuni na wannan shekara.(Tasallah)