Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 09:12:13    
Kasar Sin tana dukufa kan bunkasa wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu

cri
Tun daga ran 10 zuwa ran 18 ga wata, a birnin Guangzhou na kasar Sin, kasar Sin ta kira gasar wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu a karo na 8, wanda ke matsayin muhimmin dandamali ne na nuna al'adun wasanni na gargajiya na dukkan kananan kabilun kasar Sin. 'Yan wasa 'yan kananan kabilu da kuma kungiyoyin wakilai sun yi karawa da juna ne domin bunkasa al'adun wasannin gargajiya na kananan kabilu da kuma inganta mu'amala a tsakanin kabilu daban daban, a maimakon neman samun lambobin zinariya.

A gun gasar wasanni da aka yi a wannan karo a Guangzhou, an samar da shirye-shirye guda 15 da kuma wasu 149 na nune-nune ba tare da samun lambar yabo ba. Wadannan shirye-shirye sun sha bamban da saura bisa sigar musamman a fannonin yin gasa a tsakanin 'yan wasa da nuna fasahar 'yan wasa da kuma jin dadin kallo a idon 'yan kallo. 'Yan wasa fiye da dubu 6 da suke fitowa daga kananan kabilu 55 na kasar Sin sun shiga gasar wasannin, ba kawai sun ji murna a cikin gasar ba, har ma sun zurfafa zumunci a tsakanin kabilu daban daban.

A gun wannan gasar wasanni, dimbin 'yan wasa da jami'ai sun nuna cewa, a cikin shekarun baya, an sami babban ci gaba a fannin sha'anin wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu a wuraren da suke zama. Malam Hu Xianghua, mataimakin shugaban kungiyar wakilai ta lardin Hubei, ya gaya mana cewa,'Hukumarmu ta Hubei tana dora muhimmanci sosai kan ayyukan wasannin motsa jiki na kananan kabilu. A ko wace shekara, mun kebe kudin musamman na kudin Sin miliyan guda domin bunkasa wasannin gargajiya na kananan kabilu. Lardinmu kan shirya gasar wasannin motsa jiki na gargajiya na kanana kabilu na dukan lardin sau daya a ko wadanne shekaru 4, inda kungiyoyin wakilai 20 suka shiga, yanzu mun shirya gasanni har sau 6. Yau da shekaru 5 da suka wuce, mun kafa sansanonin bunkasa wasannin gargajiya na kakanan kabilu. Mun kara yawansu wato guda 8 a da zuwa guda 14 a yanzu. A zahiri kuma, ta haka ne muka yada wasannin motsa jiki na gargajiya na kanana kabilu.'

Baya ga Hubei, a shekarun nan da suka wuce, shiyyoyin kasar Sin da aka fi samun kananan kabilu sun sami kyakkyawan ci gaba a fannin wasannin gargajiya. Samun nasarar kiran gasar wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin a karo na 8 wani abun shaida ce mafi kyau. Malam Qi Wenxiang, mataimakin babban sakataren zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jihar Mongolia ta Gida ta kasar Sin, ya ce,'Gasar wasannin gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin ya fi wadda aka kira a da kyau, haka kuma, an fi nuna ra'ayin kirkire-kirkire a gun irin wannan gasar wasanni. Musamman ma gasar wasannin da aka yi a wannan karo, ma iya cewa, ta fi dukkan gasannin da aka taba shiryawa a da. Yawan 'yan wasa da na shirye-shirye dukkansu sun fi na da yawa.'

A shekarun baya, hukumomin kasar Sin da abin ya shafa sun yi dimbin ayyuka a fannin tono gasannin gargajiya na kananan kabilu, ayyukan da suka yi sun taka rawa mai yakini wajen tattarawa da kiyaye da kuma yada al'adun wasannin gargajiya na kananan kabilun kasar Sin.

Madam Wang Ju, mataimakin shugaban sashen yada al'adu na kwamitin kula da harkokin kabilu na kasar Sin ta yi karin bayani cewa, a gaskiya kuma, sha'anin wasannin motsa jiki na kananan kabilun kasar Sin wani irin aiki ne na kabilu. Gwamnatin Sin tana dora muhimmanci kan sha'anin wasannin kananan kabilun kasar, ta haka, ana iya ganin cewa, gwamnatin Sin tana mai da hankalinta kan ayyukan kabilu. Ta ce,'Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, dukkan kananan kabilun kasarmu sun fara tonowa da tattarawa da kuma kyautata al'adun wasannin motsa jiki na gargajiya nasu. Har zuwa yanzu dai, mun tanadi wadannan abubuwan da ke shafar al'adun wasannin gargajiya na kananan kabilun kasarmu a cikin littattafan koyarwa, wadanda ake amfani da su a jami'o'i da makarantun midil da na firamare. Shi ya sa a shekarun baya, sha'anin wasannin gargajiya na kananan kabilun kasarmu na ta samun ci gaba, haka kuma, ana ta yada su a wurare masu yawa. A birane da kuma unguwanni, a kan motsa jiki ta hanyar wasanni da 'yan kananan kabilun kasarmu suka saba bi.'(Tasallah)