Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 16:39:52    
Kasar Sin za ta kara zuba kudi kan ba da taimako ga dalibai masu fama da talauci

cri
Tun daga watan Satumba ne, aka bude jami'o'i daya bayan daya a nan kasar Sin, a shekarar da muke ciki, sabbin dalibai fiye da miliyan 5.6 na kasar Sin za su shiga jami'ai, ciki har da masu fama da talauci kusan miliyan daya. Tun daga wannan sabon lokacin karatu, kasar Sin za ta kara zuba kudi kan ba da taimako ga dalibai masu fama da talauci, haka kuma dalibai masu fama da talauci da kuma iyayensu da yawa ba za su nuna damuwa kan yadda za su biya kudin karatunsu ba. A cikin shirinmu na yau za ku ji wani bayani game da wannan.

A kauyen Zhushan na gundumar Qu ta jihar Sichuan da ke yammacin kasar Sin, wakilinmu ya gamu da Xu Chenxi, wata yariniyar da ke da shekaru 17 na haihuwa, da kuma iyalinta. A wancan lokaci, suna shara a gidansu da ya rushe. Saboda kwanan baya, an samu ambaliyar ruwa a kauyen, a sakamakon haka, iyalin Xu Chenxi ya fi shan wahala bisa na da. Yaya za a shirya kudin karatu na Xu Chenxi wajen shiga jami'a? Wannan dai ya zama muhimmiyar matsalar da iyalin nan ke fuskanta.

Har zuwa yanzu aikin ba da ilmi a jami'o'i na kasar Sin ba na tilas ba ne, saboda haka ne, ko wane dalibin jami'a zai kashe kudi kamar RMB dubu goma wajen kudin karatu, da kwana da kuma zaman rayuwa a ko wace shekara. Lallai wannan babban nauyi ne da ke bisa wuyan wani iyali mai fama da talauci, musamman ma na kauyuka.

Amma, da sauri aka warware wannan matsalar da iyalin Xu Chenxi ke fuskanta. Ba kawai hukumomin harkokin jama'a da na ba da ilmi na wurin sun bayar da taimakon kudi a fannin karatu da yawansu ya kai RMB dubu 6 ga Xu Chenxi ba, har ma sun bayyana masa sabbin manufofin ba da taimako a fannin karatu ta kasar. Mr. Xiong Changhong, shugaban hukumar ba da ilmi ta gundumar Qu ta jihar Sichuan ya ce:

"Bayan da dalibai suka shiga jami'a, za su samu taimako daga sabbin manufofin ba da taimako a fannin karatu na kasar. Wasu daga cikinsu suna da damar samu kudin bonas da kasar ta bayar, wato dalibin da zai zai samu kudin RMB dubu biyar a ko wace shekara. Wadanda masu fama da talauci kuma za su samu taimakon kudi a fannin karatu. Bayan haka kuma, wasu dalibai suna iya samun taimakon kudi ta ayyukan da suka yi, a waje daya kuma kasar za ba da rancen kudi na taimako ga dalibai."

A hakika dai, kullum kasar Sin tana kokari don kafa wani tsarin ba da taimakon kudi mai hanyoyi da dama. Amma, a cikin daliban jami'a kusan miliyan 17 na kasar Sin, wadanda masu fama da talauci sun kai kashi 20 cikin dari, lallai sun yi yawa, saboda haka, ba dukan dalibai ke iya samun taimakon kudi ba, wasu daga cikinsu ba su iya kammala karatunsu domin rashin isasshen kudi. Don warware wannan matsala, tun daga wannan sabon lokacin karatu, kasar Sin za ta kara bayar da kudi kan taimakawa dalibai masu fama da talauci. Mr. Zhao Lu, shugaban hukumar ba da ilmi da kimiyya da al'adu na ma'aikatar kudi ta kasar Sin ya gabatar da cewa:

"A wannan lokacin karatu, gwamnatocin tsakiya da na wurare daban daban za su bayar da kudi RMB biliyan 15.4 don aiwatar da sabbin manufofin ba da taimako a fannin karatu, amma a da yawan kudin da aka yi amfani da su kan taimakon kudi ya kai biliyan 1.8 kawai."

Ban da manufofin ba da taimakon kudi, kuma gwamnatocin wurare daban daban na kasar Sin sun ma sun ba da manufofin ba da taimako a fannin karatu da kansu. Kamar misali, a gundumar Qu da Xu Chenxi ke zaune, gwamnatin wurin ta ba da taimakon kudi ga dalibai masu fama da talauci bisa hakikanan halin da suke ciki. Mr. Zhang Di, wani jami'in gwamnatin wurin ya gayawa wakilinmu cewa:

"Gwamnatin gungumarmu ta aiwatar da shirin ba da taimako ga dalibai masu fama da talauci a dukan fanoni, duk dalibai masu fama da talauci na gundumar Qu da suka shiga jami'o'i, za su samu taimakon kudi RMB fiye da dubu biyu, hakan za su iya shiga jami'o'i lami lafiya."

Mun sami labari daga ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin cewa, kara karfin taimaka wa dalibai masu fama da talauci a fannin karatu a sabon lokacin karatu, wannan ne mataki na farko kawai, a 'yan shekaru masu zuwa, yawan kudin da gwamnatin kasar za ta bayar domin taimakawa dalibai masu fama da talauci zai kara karuwa har zuwa RMB biliyan 50, a lokacin can dalibai kusan miliyan hudu za su samu moriya daga cikin a ko wace shekara.( Bilkisu)