Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-26 16:08:46    
Masana'antun gwamnatin Sin na gaggauta daukar matakai wajen tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli

cri
A cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta yi ta bunkasa harkokin tattalin arzikinta ne cikin sauri sosai, amma sabanin da ta samu wajen bunkasa tattalin arziki da kiyaye muhalli kullum sai kara tsanani yake yi. Don daidaita wannan sabani, kasar Sin ta tsara manufarta game da tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa cikin wani matsakaicin lokaci, ta yadda za ta sami ci gaba mai dorewa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Bisa matsayinsu na ginshikin tattalin arzikin kasar Sin, manyan masana'antun gwamnatin kasar sun nuna himma wajen mayar da martani ga kirar da gwamnatin kasar ta yi musu, sun gaggauta daukar matakai wajen tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurbata muhalli da suke fitarwa.

A kwanakin baya, yayin da Malam Xie Zhenhua, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin yake halartar wani taron dandalin tattaunawa kan ayyukan tsimin makamashi da na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, ya bayyana cewa, "manyan ayyuka da muke yi a yanzu su ne, na daya, a inganta tsarin sanya ido kan ayyukan tsimin makamashi da na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli; na biyu, a tsaya tsayin daka wajen rage saurin karuwar masana'antu wadanda ke bukatar makamashi mai yawa da fitar da dimbin abubuwa masu gurbata muhalli; na uku, a rubanya kokari wajen rufe tsoffin masana'antu da ke da koma baya; na hudu, a gaggauta yin manyan ayyukan tsimin makamashi da na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli; na karshe, a bukaci manyan sana'o'i da manyan masana'antu da su yi tsimin makamshi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sosai."

A hakika dai, yawancin masana'antun gwamnatin kasar Sin suna mai da hankali sosai ga aikin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurtaba muhalli. Kamfanin goran ruwa na kasar Sin kamfanin karafa ne mafi girma a kasar Sin. Malam Lu Youqing, mataimakin babban manajan kamfanin ya bayyana cewa, yanzu, kamfaninsa ba ya fitar da gurbataccen ruwa ta hanyar zamani. Ya kara da cewa, "a shekarar 2006, nauyin ruwan da masana'antun kamfaninmu suka sake yin amfani da shi ya kai kashi 88 cikin dari. Haka kuma nauyin ruwan da suka yi amfani da shi wajen kara narkar da goran ruwa ya ragu da kashi 35 cikin dari a shekarar nan bisa na shekarar 2005, dadin dadawa masana'antunmu da yawa ba su sake fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ba."

Ana bukatar makamashi mai yawa wajen samar da wutar lantarki. Malam Wu Nuosi, mataimakin babban manaja na babban kamfanin makamashi mai suna Huaneng na kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kasar Sin tana samar da wutar lantarki ne musamman ta hanyar kwal, amma sabo da rashin samun isassun kudade da fasahar zamani, kasar Sin ta dade tana bukatar kwal mai dimbin yawa wajen samar da wutar lantarki, wanda kuma ke gurbata muhalli sosai. Ya kara da cewa, kullum kamfaninsa yana mai da hankali sosai ga samar da wutar lantarki ta hanyar zamani. Yau a shekaru uku da suka wuce, kamfaninsa ya gabatar da shirin samar da wutar lantarki ta hanyar kwal kuma ba tare da gurbata muihalli ba. Ya ce, "bisa shirin, za mu daga matsayin kamfaninmu sosai na yin amfani da kwal a fannoni daban daban, sa'an nan kamfaninmu ko kusa, ba zai fitar da hayaki da sauran abubuwa masu gurbata muhalli ba, ta haka abubuwa masu gurbata muhalli da hayaki mai daumama yanayi da kamfaninmu ke fitarwa sun ragu sosai. "

Kwararru sun nuna cewa, ta hanyar tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, ba ma kawai manyan masana'antun gwamnatin kasar Sin suna ba da taimako wajen tsimin albarkatun kasa da kyautata muhalli ba, har ma sun rage yawan kudi da suke kashewa wajen samar da kayayyaki. (Halilu)