---- A ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, an kafa kwamitin shirin babban wasan motsa jiki na gargajiya na karo na 8 na kananan kabilun kasar Sin a hukunce.
Za a yi babban wasan motsa jiki na gargajiya na karo na 8 na kananan kabilun kasar Sin daga ran 10 zuwa ran 18 ga wannan wata a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin. A lokacin kuwa, da akwai kungiyoyin wakilai 34 wadanda za su zo daga wurare daban- daban na kasar Sin wadanda kuma ke kunshe da 'yan wasan kananan kabilu da yawansu ya wuce 6,300 za su shiga wannan babban wasan motsa jiki.
Za a yi gasanni iri 15 da sauran wasanni ira 148 da ba na yin gasa ba a gun wannan babban wasan motsa jiki. An ce, kungiyar wakilan 'yan kananan kabilun lardin Taiwan za ta nuna wasanni iri 6 daga cikin wasannin da ba na yin gasa ba, ban da wannan kuma za ta shiga gasa a koro na farko wato gasar yin kokawa irin na kabilu.
---- An yi wani manomi Nimaciren a garin Dazi na gundumar Linzhi ta jihar Tibet ta kasar Sin wanda yake da shekaru 22 da haihuwa ya tsai da wani jadawalin nuna wasanni, kowace rana da dare, daga karfe 6 da rabi zuwa karfe 8 da rabi yakan yi rawar gargajiya ta kabilar Tibet a wani kauyen al'adun gargajiya na gundumar Linzhi domin masu yawon shakatawa, daga karfe 9 zuwa karfe 10 da dare kuma yakan je wani dakin shan giya domin yin rawa tare a lokacin da ake waka, daga karfe 10 da rabi da dare zuwa karfe 2 na kashegari da asuba kuma yakan tafi dakunan wake-wake da raye-raye irin na kabilar Tibet guda 2 bi da bi don nuna wasanni.
Ko da yake Mr. Nimaciren ya jaji tikis, amma yana jin dadi sosai ga irin wannan aikin da yake yi yanzu, ya ce, "Da ma ina son yin waka da rawa, kuma yanzu a kowace rana ina nuna wasanni a wurare da yawa, shi ya sa kudin shiga da na samu ya fi na aikin noma yawa nisa ba kusa ba."
Kafin rabin shekarar da ya zuwa, Mr. Nimacire ya yi aikin noma a garinsa, yawan kudin shiga da ya samu kadan ne, amma yanzu yawan kudin shiga da ya samu daga wajen wasannin da ya nuna a kauyen al'adun gargajiya kawai ma ya wuce kudin Sin wato Yuan 1,000 a kowane wata.
A jihar Tibet na kasar Sin, da akwai manoma da makiyaya da yawa wadanda ke yin zamansu tamkar Mr. Nimaciren, sun nuna halin musamman nasu na kwarewa wajen yin rawa da waka, suna fadi tashi a dandalin wasa iri daban-daban, a lokacin da suke nuna wasannin gargajiya domin 'yan kallon da suka zo daga wuraren jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da sauran wurare daban- daban, yawan kudin shiga da suka samu shi ma yana ta karuwa. An ce, yawan mutanen da suka je jihar Tibet domin yawon shakatawa daga watan Janairu zuwa ta Satumba na wannan shekara ya wuce miliyan 3.2, wato ya wuce yawan mutanen jihar da yawansu ya kai miliyan 2.81.
Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)
|