
Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai wadda ta kafu a shekara ta 1958 tana daya daga cikin jihohi biyu na kananan kabilu masu cin gashin kai na kasar Sin, tana da'kalibar Hui da ke bin addinin Musulunci fiye da miliyan 2, sabo da haka kafofin watsa labarai na kasashen waje su kan kira jihar Ningxia da sunan "jihar musulmai ta Sin". Haka kuma al'adun gargajiya da tarihin musulmi na dogon lokaci sun jawo hankulan mutane masu yawon shakatawa na gida da na waje.

Yau na je wurin shan iska na al'adun musulmi da ke gundumar Yongning ta birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia domin yawon shakatawa. Da zarar na isa wurin, nan da nan gine-ginen da ke da halin musamman na musulunci sun jawo hankalina sosai.

An gina wannna wurin shan iska ne da ke da halin musamman na musulunci bisa tallafawar musulmai da ke nuna kauna ga al'adun musulunci da kuma gwamnatoci na matakai daban daban na kasar Sin, haka kuma shi wuri daya tak a kasar wajen nuna al'adun gargajiya na kabilar Hui.

Bayan da na shiga babbar kofa, sai na ga wani dakin nuna kayayyakin tarihi na kabilar Hui da ke cibiyar wannan wurin shan iska, inda ake iya ganin kayayyakin tarihi masu dimbin yawa da aka nuna wajen tarihin kabilar Hui ta kasar Sin, da yunkurin shimfida wayin kai na musulunci, da al'adun gargajiya na kabilar Hui, da babbar gudummowar da kabilar Hui ta bayar a tarihin kasar Sin, da kuma bunkasuwar kabilar Hui ta jihar Ningxia.
Sabo da haka, ana iya ganin cewa, lalle wurin shan iska na al'adun kabilar Hui na kasar Sin wani muhimmiyar shaida ce wajen yada wayin kai na musulunci, da sa kaimi ga cudanyar aminci tsakanin kabilu da kasashe da kuma shiyya-shiyya, da kuma hadin gwiwar kabilun kasar Sin.
|