Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-23 18:02:50    
Kasar Sin za ta raya sabon makamashi a yankunan karkara

cri
A ran 23 ga wata a nan birnin Beijing, ofishin ba da jagoranci kan harkokin makamashi na kasar Sin da hukumar tsara shirin neman bunkasuwa ta majalisar dikin duniya sun yi taron kasa da kasa na kara wa juna sani kan yadda za a raya sabon makamashi a yankunan karkara na kasar Sin. Jami'an gwamnatin kasar Sin sun ce, gwamnatin tana taimakawa yankunan karkara da su yi amfani da makamashi mai tsabta da za a iya sake yin amfani da shi, kamar su karfin hasken rana da karfin iska da dai sauransu.

A gun taron, Mr. Ma Fucai, mataimakin shugaban ofishin ba da jagoranci kan harkokin makamashi na kasar Sin yana ganin cewa, ko da yake kasar Sin ta samu cigaba sosai wajen raya makamashi a yankunan karkara a cikin shekaru da yawa da suka gabata, amma tana kuma fuskantar sabon kalubale. Ya ce, "Da farko dai, yawan makamashin da aka yi amfani da su a yankunan karkara bai yi yawa ba, yawan makamashin da kowane mutum yake amfani da shi ya kai sulusi kawai bisa yawan makamashin da kowane mazaunan birni yake amfani da shi. A waje daya kuma, har yanzu manoma suna da al'adar yin amfani da katako lokacin da suke girki da dumama daki. Bugu da kari kuma, ayyukan yau da kullum na samar da sabon makamashi a yankunan karkara sun koma baya, manoma ba su iya samun isashen makamashi mai tsabta da suke bukata. Haka kuma, yankunan karkara na kasar Sin sun fi birane bukatar makamashi a cikin dogon lokaci mai zuwa."

Ma Fucai ya ce, kwal da man fetur da ake amfani da su yanzu suna da wahalar biyan bukatun da yankunan karkara suke nema domin raya tattalin arziki da zaman al'ummarsu, haka kuma za su kawo illa ga muhalli. Sabo da haka, a gun taron, Mr. Wu Guihui, mataimakin direktan hukumar kula da harkokin makamashi a kwamitin yin gyare-gyare da neman cigaban kasar Sin ya ce, game da batutuwan karancin makamashi mai tsabta da ake kokarin daidaitawa a yankunan karkara na kasar, gwamnatin kasar Sin tana gaggauta tsara shirin raya makamashi a yankunan karkara. A waje daya kuma, za ta kara saurin shimfidawa da yin kwaskwarima kan tsarin samar da wutar lantarki domin kara karfin samar da wutar lantarki a yankunan karkara. Sakamakon haka, yawan manoman da za su iya yin amfani da wutar lantarki zai iya samun karuwa.

Wu Guihui ya bayyana cewa, raya sabon makamashi hanyar da ta wajaba wajen daidaita batun makamashi a yankunan karkara na kasar Sin. Ya kuma gabatar da matakan da za a dauka wajen raya sabon makamashi a yankunan karkara. Ya ce, "Za a kara saurin yada fasahohi masu arha kuma masu mafani na yin amfani da makamashin da za a iya sake yin amfani da su. A waje daya kuma, za a ci gaba da taimakawa manoman da suke kiwon dabbobi da su gina ramukan iskar gas da aka samu daga taki. Sannna, za ta sa kaimi kan yankunan da suke da karfin hasken rana da su yi amfani da fasahar samar da wutar lantarki da injunan samar da ruwan zafi da injunan girki da karfin hasken rana domin rage yawan katako da kwal da ake amfani da su a yankunan karkara da kyautata muhallin yankunan karkara da kuma kyautata ingancin zaman rayuwar manoma. "

A cikin nasa jawabin, Mr. Subinary Nandy, direktan ofishin hukumar tsara shirin neman bunkasuwa ta majalisar dinkin duniya, wato UNDP da ke nan kasar Sin ya dauki alkawarin cewa, hukumar za ta ci gaba da yin hadin guiwa da kasar Sin, kuma za ta taimaki kasar Sin a fannonin kudade da fasahohi domin raya makamashi yankunan karkara na kasar. Mr. Subinary Nandy ya ce, "A cikin shekaru 10 da suka gabata, mun riga mun zuba kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 75 kan shirye-shiryen raya makamashin da za a iya sake yin amfani da su a yankunan karkara na kasar Sin. Muna raya shirin amfani da karfin hasken rana a yankunan yammacin kasar domin babu isassun tsare-tsaren samar da wutar lantarki a yankunan, amma hasken rana ya yi yawa." (Sanusi Chen)