Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-23 16:16:45    
Babbar ganuwa ta kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam mamane Ada, mai sauraronmu daga birnin Yamai da ke jamhuriyar Nijer. Malam Mamane Ada ya turo mana wasika a kwanan baya cewa, A gaskiya dandalinku na amsoshin tambayoyin masu saurare na da mahimmanci sosai da sosai?domin haka ne nike fatan ku share mani hawaye dangane da abin dake damu na a game da neman cikaken tarihin wannan ganuwa ta 'muraille de la chine', tambayoyin su ne a wane lokaci ne aka gina ta, sabo da me aka gina ta, shin da gaske ne idan ana duniyar wata wannan ganuwa ce ake hange? Ba ma kawai shi malam Mamane Ada ya turo mana wadannan tambayoyi dangane da babbar ganuwa ta Sin ba, a hakika, masu sauraronmu da yawa sun sha turo mana tambayoyinsu dangane da babbar ganuwar Sin, misali?Rabiu Ibrahim Fagge wanda bai bayyana cikakken adireshinsa ba, ya rubuto mana cewa, ku ba ni tarihin katangar china, a wace shekara aka gina ta, waya gina ta, shekaru nawa aka yi ana gina ta? A sabili da haka ne, masu sauraro, ko da yake da ma mun taba kawo muku tarihin wannan babbar ganuwa ta kasar Sin a wannan filinmu na Amsoshin wasikunmu, idan ba ku manta ba, amma yau bari mu kara muku bayani a kan ganuwar, domin amsa tambayoyin masu sauraronmu.

Babbar ganuwa ta kasar Sin wani babban aiki ne da aka fi jimawa ana yinsa domin tsaro a kasar Sin har ma a duk fadin duniya. Tun daga karni na bakwai kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam ne, aka fara gina wannan babbar ganuwa. Daga bisani, an yi shekaru har 2000 ana ta gina ta. Wannan babbar ganuwa kuwa, ta shimfidu ne a filaye masu yawa da ke arewacin kasar Sin da kuma tsakiyarta, kuma tsawonta ya kai kilomita sama da dubu 50 gaba daya. Babban aiki kamar ta a kasar Sin ita kadai, ko a duk duniya ma ba za a samu wani daban ba. Sabo da haka, an sa ta cikin manyan ayyuka 7 masu ban mamaki na duniya a shekaru daruruwa da suka gabata.

Muna iya bin asalin babbar ganuwa daga karni na 9 kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam, wato a zamanin daular Xizhou na kasar Sin. A lokacin, daular Zhou ta gina wasu gine-gine a jere don kare harin makiyaya daga arewa. Ya zuwa karni na bakwai kafin haihuwar annabi Isa, wato a zamanin Chunqiu da kuma zamanin yake-yaken dauloli na kasar Sin, dauloli daban daban sun sha yin takara da juna, kuma sun yi ta gina ganuwa a kan iyakarsu, domin tsaron kansu da kuma magance hari daga sauran dauloli. Amma ganuwar da aka gina a lokacin gajere ne, kuma tsawonsu ya kai kilomita daruruwa zuwa dubu daya ko biyu ne kawai.

Daga baya, a shekara ta 221 kafin haihuwar Annabi Isa kuma, sarki Qinshihuang ya murkushe sauran dauloli shida, kuma ya harhada duk kasar Sin baki daya a karkashin mulkinsa. Domin neman magance hari daga makiyaya 'yan kabilar Xiongnu da ke arewa, sai ya habaka babbar ganuwar bisa tsoffin ganuwar da aka rigaya aka gina, ta yadda za a inganta tsaron kasa da kuma kwanciyar hankali. Bayan sarki Qinshihuang, dauloli daban daban suka yi ta ci gaba da gyaran babbar ganuwa da kuma habaka ta. Musamman ma a zamanin daular Han da Jin da kuma Ming, babbar ganuwa ta fi habaka, har ma tsawonta ya kai kilomita dubu 5 ko kuma dubu 10.

Babbar ganuwa ta kasar Sin wadda ke da tsawon kilomita dubu 50, ba wai kawai wata ganuwa ba ce, amma wani cikakken tsari ne na tsaro wanda ke kunshe da katangu da gine-ginen ba da alamar yaki da gine-ginen soja da dai sauran gine-gine na tsaro.

Sa'an nan, a game da tambayar nan, shin da gaske ne idan ana duniyar wata wannan ganuwa ce ake hange? A hakika, da ma akwai littattafan da suke bayanin cewa, ana iya hangen wannan babbar ganuwa daga sararin samaniya, amma a cewar malam Yang Liwei, wani dan sama jannati na kasar Sin wanda ya taba zuwa sararin samaniya, bai ga ganuwar ba. Bayan haka, masanan kimiyya su ma sun tabbatar da cewa, a sararin sama da ke da nisan kilomita 300 daga doron kasa, idanun dan Adam na iya ganin abin da fadinsa ya wuce mita 500, amma ga shi fadin ganuwar Sin na da mita 10, sabo da haka, a sararin sama da ke da nisan kilomita 36 ne kawai, babbar ganuwar Sin za ta bace a idanunmu, balle ma a ce ana iya ganinta a sararin samaniya ko kuma duniyar wata da ke da nisan kilomita dubu 384.(Lubabatu)