Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-23 16:06:29    
Gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya da CRI ta gudanar a game da taron wasannin Olympics na Beijing (babi daya)

cri

Ana gudanar da ayyukan share fagen taron wasannin Olympics na Beijing lami-lafiya

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuke sanin cewa, za a gudanar da taron wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 tsakanin ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Domin samar muku da wata kyakkyawar damar kara samun ilmi da kuma sa hannu cikin harkokin taron wasannin, tun daga yau wato ran 9 ga watan da muke ciki, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya kaddamar da gasar ka-cici-ka-cici a fadin duk duniya a game da ilmin taron wasannin Olympics na Beijing, wadda ke da lakabi haka: " Mu yi haduwa a shekarar 2008" ta hanyar yin amfani da harsunan waje 38, da Sinanci, kare-karen harsuna iri 4 na wuraren kasar Sin da kuma tashar internet wato www. cri.com.cn.

Gasar nan za ta dauki rabin shekara. A cikin wannan lokaci dai, za mu watsa bayanan musamman guda 4 na game da taron wasannin Olympic daya bayan daya; kuma a karshen kowane bayanin musamman, akwai tambayoyi guda biyu game da taron wasannin. To, za ku iya shiga wannan gasa ta hanyar sauraron shirye-shiryenmu. Abin da ya fi burge aminai masu sauraronmu shi ne, duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman, za su iya kawo ziyara nan Beijing a watan Yuni na shekara mai zuwa.

Yanzu bari in karanto muku bayanin musamman na farko wanda ke da lakabi haka: "Ana gudanar da ayyukan share fagen taron wasannin Olympics lami-lafiya".

Jama'a masu sauraronmu, idan dai ba ku manta ba, tuni a ran 13 ga watan Yuli na shekarar 2001, gwamnatin birnin Beijing ta cimma burin samun iznin gudanar da taron wasannin Olympics na yanayin zafi a shekarar 2008. Cikin shekaru 6 da suka shige, gwamnatin birnin ta sanya matukar kokari wajen share fagen taron wasannin Olymmpics na Beijing. Mataimakin shugaban zartarwa na kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing Mr. Wang Wei ya furta cewa: " Gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympics mai matsayin koli dake da sigar musamman a shekarar 2008, alkawari ne da muka dauka ga kasashen duk duniya, kuma babban buri ne na gwamnatin kasar Sin da jama'arta. A takaice dai, ana gudanar da ayyukan share fagen taron lami-lafiya".

Jama'a masu sauraro, ayyukan share fagen taron wasannin Olympics na Beijing sun samu goyon baya daga mazauna birnin Beijing da kuma jama'ar kasar Sin. Alal misali: yawan mutanen da suka yi rajistar zama masu aikin sa kai domin wannan gagarumin taron wasanni ya rigaya ya zarce 500,000 duk da cewar ana bukatar mutane kimanin 100,000 kawai, kuma yawan wadanda suka yi rajista daga babban yankin kasar Sin ya dauki kashi 90 cikin kashi 100 bisa jimlar mutanen da suka yi rajista. Lallai zafin nama da jama'ar kasar Sin suka nuna ya bada alama mai gamsarwa ga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa. Mr. Wang Wei ya bayyaa cewa: " Yansu ana gudanar da ayyukan daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympics da kuma taron wasannin Olympics na nakasassu a larduna da birane da kuma jihohi masu cin gashin kai guda 31 na babban yankin kasar Sin. Ban da wannan kuma, an soma gudanar da irin wannan aiki daga dukkan fannoni a yankin Hongkong da Macao da kuma na Taiwan da dai wasu yankunan ketare. Ya zuwa karshen watan Yuli na shekarar 2007, yawan mutane daga wadannan yankuna da suka yi rajistar ya wuce 560,000."

Aminai masu sauraro, ko kuna sane da cewa, duk wani birnin dake daukar bakuncin taron wasannin Olympics, wajibi ne yana da kyakkyawan yanayin sufuri da na zirga-zirga da kuma kyakkyawan muhalli. Ko shakka babu gwamnatin birnin Beijing ta samu babbar nasara a wadannan fannoni biyu.

A sa'I daya kuma, gwamnatin birnin Beijing ta samu sakamakon a-zo-a-gani wajen kyautata muhallin birnin. Daga shekarar 1998 zuwa shekarar 2006, gwamnatin birnin ta zuba makudan kudade da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan goma sha biyu da miliyan dari biyu wajen kara kyautata ingancin iskar sararin samaniya, da dasa bishiyoyi da ciyayi da kuma tsabtace kazantaccen ruwa. Mr. Wang Wei yana mai cewa: " an kara samun kyautatuwar yanayin sufuri da zirga-zirga da kuma muhallin halittu a nan Beijing yayin da ake aiwatar da hasashen ' gudanar da taron wasannin Olympics cikin kyakkyawan yanayi', sa'annan kuma an kara samun jituwa tsakanin al'ummomin kasar"

A karshe dai, Mr. Wang ya ce, yanzu lokaci bai kai shekara guda ba a gudanar da bikin bude taron wasannin Olympics na Beijing. Don haka, nan gaba gwamnatin birnin Beijing za ta gaggauta ayyuka na fannoni da dama bisa yadda aka saba yi tsakanin kasa da kasa a gun tarurrukan wasanin Olympics na da kuma bisa ra'ayoyi da shawarwari iri daban-daban da gwamnatin kasar Sin ta gabatar a game da wannan gagarumin taro. (Sani Wang )