Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-22 17:33:17    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (8)

cri

---tsofafi guda biyu suna sayar da abinci:An sami wani tsoho da ake kiransa Mr Zhang wanda ya ke da shekaru 83 da haihuwa da matarsa 82 suka kafa wani dakin cin abinci bayan da suka yi ritaya maimakon sun yi hutu a gida.Mr Zhang shi kuku ne ya kware wajen dafa abinci sabo da kakakaninsa ma masu dafa abinci ne ta haka ya san asirin dafa abinci mai dadi,Dakin cin abincin da ya kafa ya yi suna a wurinsa mutane da yawa su kan ci abinci a can.Matarsa sabis ce a cikin wannan dakin.

---Baki sun sami taimako daga tsofafi na wuri.Da akwai tsofafi goma da suka ji turanci sun zama masu sa kai.A lokacin da ake bukukuwan murnar bikin kasa,sun ba da taimako ga baki da suka zo nan kasar Sin domin yawon bude ido.Bakin da suka sami taimakonsu sun wuce dari shida.Sun kuma samu yabo daga baki da mutnen wurin har kwamitin kula da unguwa ya yi musu yabo sabo da ayyukan da suka yi.

---Kare na kula da tsuntsu da mai gida.An sami wani mutum a birnin Changchun na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin yana kishin wasannin motsa jiki,ya kuma yi kiwon wani kare.Da kare ya girma ya yi aiki dominsa.Shi mai kishin wasa ya kuma nada wani kejin da ya sa tsuntsu a ciki.Duk yayin da ya ke wasan motsa jiki,sai karensa ya zauna wajen sa ya sa lura kan mai gida da kuma kejin da aka sa tsuntsu a ciki.Idan wani mutum ya kusanci kejin sai karen ya yi fushi.

----An kama wasu mazambata a Hongkong.'Yan sanda a Hongkong sun kama mutane uku da ake tuhumarsu ke da hannu a makarkashiyar "Ponzi" da aka kulla,an tabbatar da makarkashiya ne ta hanyar yanar internet.wato ta hanyar zuba jari ta internet.Su kan cui masu amfani da yanar Internet,da cewa idan suka shiga wani shirin zuba jari.za a iya mayar da ruwan kudin jari da kashi 25 bisa dari,da mazambata sun samu wasu kudi suna neman su bace.duk da haka 'yan sanda sun sami labarinsu kafin su tsira.

---Wata mata ta isa abin misalin koyo a lardin Shaanxi na kasar Sin.An sami wata mata da shekarunta ya kai hamsin da haihuwa.Ta auri wani namiji mai suna Li Junfeng.Bayan da suka yi aure,'yan'uwan Li biyu sun sami tabin hankali.Surukinta ya nuna damuwa kan batun nan sosai.Da ya ke fama da ciwo mai tsanani,hankalinsa bai kwanta ba saboda 'ya'yansa biyu.sai ta kirawo matar dansa da ta kula da 'ya'yansa.Matar ta alkawarta za ta dauki nauyi bisa wuyanta na kula da su.Bayan rasuwarsa Matar ta kula da 'ya'yansa cikin shekaru 22 da suka gabata.Ita da mijinta sun yi aiki tukuru sun sama da abinci da tufafi da dakunan kwana domin su,har ma sun taimakonsu wajen aure da kula da yara.Matar ta samu yabo sabo da ayyukan nagarta da ta yi cikin tsawon shekaru sama da ashirin.

-----Wani tsohon jami'in soja ya samu yabo daga jama'a.Wani jami'in soja da ya yi ritaya ya koma gida,da ya ga halin da kauyensa ke ciki,sai hankalinsa ya tashi,ya niyyata zai yi wani abu domin canza wannan hali.Sunan jami'in soja shi ne Du Fangxiu.yana zaune a gundumar Dingbian na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin inda hamada ta fi gagara.A cikin shekaru talatin da suka shige,ya kashe dukkan kudin da ya samu wajen kyautatta muhalli.Ya ce "na sami kudi ne ta hanyar da sayar da amfanin gona.Da kudin da na samu ne,zan dasa itatuwa da ciyayi a kan duwatsu marasa tsirai".Bisa jagorancinsa,mutanen da suka fito daga kauyuka 153 sun shiga aikin mayar da wuri mai fako na kadada dubu goma wuri mai ciyayi da itatuwa.

----Wani mutum da tsuntsayensa:An sami wani tsoho mai yawan shekaru 80 da haihuwa da ake kiransa Mr Zhang a birnin Xi'an na lardin Shaanxi na kasar Sin. Yana kishin tsuntsaye har ya kan fita waje domin samar da abinci ga tattabara da gwara. Ko wace rana da safe ya kan fita ya je lambun shan iska na dab da babbar ganuwa,a wurin nan tattabara da gwara kimanin metan su kan taru suna yi masa maraba da cin abincin da ya kawo musu. Tsohon ya ce "Daga shekara ta 2003 ne na fara bayar da abincin ga tsuntsaye saboda ba su da isashen abinci.A cikin shekaru uku na baya,masu yawon shakatawa da mutanen wurin sun ba da taimako su ma samar da abinci ga tsuntsayen.A ganina kamata ya yi Bil Adam da tsuntsaye su yi zama tare cikin lumana."

---Wani namiji ya auri mata a hukunce bayan shekaru 43. Wani namiji da wata mata sun yi aure a hukunce kafin ranaikun bukin kasa bayan da suka yi zama tare cikin shekaru 43 da suka gabata.

Namijinn nan sunansa Yang Dayou,yana da shekaru 71 da haihuwa,matar tana da shekaru 66 da haihuwa.A can da ana haramta musu aure ne saboda a ganin iyayen matar,iyalin mijinta na da tarihi maras kyau.Duk da haka sun yi zama tare kuma sun haifr da 'ya'ya guda hudu.

---Wani mutum ya tsaya kan yatsunsa biyu.Wani mutum da ya yi wasan gargajiya na kasar Sin wato Qigong,yanzu yana iya tsayawa kan yatsarsa daya na hannun dama da na hannun hagu,yana neman shahararen littafin Guiness na daukar bayanan abubuwa masu mamaki na duniya da ya tabbatar da aikinsa.Sunan mutum Zhang Xiong,yana da shekaru 40 da haihuwa.A da ba shi da koshin lafiya sabo da aka yi masa fida.daga baya ya yi wasan gargajiya na kasar Sin Qigong a shekara ta 2001 domin inganta lafiyarsa.Bayan shekaru shida ya kware wajen wasan har ma yana iya tsayawa a kan yatsunsa biyu.ya kago wani abin mamaki a duniya.