Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-22 14:35:03    
Da kyar Afircom ta iya zaunad da gindinta a Afirka

cri

A kwanan baya, gwamnatin kasar Nijeriya ta ki amincewa da ofishin ba da umurni na sojojin Amurka a Afirka wanda ya kafu ba da jimawa ba, da ya zaunad da gindinta a kasar. Wato ke nan rundunar sojojin Amurka ta sake shan kaye a kan batun zaben wurin ofishinta na ba da umurni a Afirka.

Har kullum, gwamnatin kasar Nijeriya na kin amincewa da sojojin Amurka da su kafa ofishinsu na ba da umurni a Afirka. A ranar 19 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Nijeriya, Umaru Yar 'adua ya yi taro tare da 'yan majalisar dokoki tare kuma da gwamnonin johohi daban daban na kasar, don yin shawarwari a kan batun. Bayan taron, gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki ya sanar da cewa, ban da kin amincewa da sojojin Amurka da su kafa ofishinsu a yankin Nijeriya, Nijeriya ita ma tana kin yarda da kafa shi a sauran kasashen yammacin Afirka.

A watan Faburairu na shekarar da muke ciki, shugaba Bush na Amurka ya amince da shirin kafa ofishin ba da umurni na sojojin Amurka a Afirka, kuma a ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki, sojojin Amurka sun sanar da kafuwar ofishin a hukunce. Amma duk da haka, kasashen Aljeriya da Morroco da Libya da Uganda da kuma wasu kasashe 14 na kungiyar SADC, wato kungiyar raya kudancin Afirka, a fili ne suka bayyana cewa, ba su son zama wurin da za a kafa ofishin ba da umurni na sojojin Amurka a Afirka ko kuma samar wa sojojin Amurka dadadden sansani.

A yayin da yake hira da manema labarai, wani jami'in ma'aikatar tsaron Nijeriya ya bayyana cewa, "sha'awar da gwamnatin Amurka ta nuna wa Gulf din Guinea ta tilasta wa Nijeriya da ta dauki tsauraran matakai, don tabbatar da tsaron shiyyar yadda ya kamata." Ya kuma yi nuni da cewa, a ganin shugabannin Nijeriya, barazanar ta'addanci da hukumar Amurka ke shelarta makarkashiya ce kawai, wanda ke kan yunkurin kafa sansanin sojojin Amurka. Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Nijeriya na ganin cewa, makasudin mahukuntan Washington shi ne kwace mai. Don kada Amurka ta mallake albarkatun kasa na shiyyar, gwamnatin Nijeriya ta riga ta yi shawarwari tare da shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka da na kungiyar ECOWAS, inda suka tattauna yadda za su iya hana Amurka da ta girke sojojinta da yawa a gulf din Guinea.

A hakika dai, akasarin kasashen Afirka ba su da aminci ga kafa sansani da sojojin Amurka za su yi a Afirka. Na farko dai, suna damuwa kan lalata cikakken mulkin kansu da za a yi. A ganinsu, bayan da sojojin Amurka suka kafa ofishinsu da kuma girke dimbin sojoji a nahiyar Afirka, tabbas ne za su tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, wanda zai lalata mulkin kan kasashen da kuma ikonsu kan albarkatun kasa.

Na biyu kuwa, duk da kalaman da jami'an Amurka ke yi a kan huldar abokantaka da ke tsakanin Amurka da Afirka, kasashen Afirka na ganin cewa, makasudin Amurka shi ne moriyar kanta. Sabo da a shekarar 2006, Afirka ta riga ta wuce gabas ta tsakiya, har ma ta zama wuri mafi muhimmanci da Amurka ke shigar da gurbataccen mai. A yanzu haka dai, Amurka na shigar da gurbataccen mai da yawansu ya kai kimanin ganguna miliyan 1 da dubu 500 a kowace rana daga Nijeriya da Angola da sauransu.

Bayan haka, yanzu yawancin ayyukan ta'addanci ana gudanar da su ne kan Amurka da kuma wasu kasashen yammaci, shi ya sa kasashen Afirka na damuwa cewa, idan Amurka ta kafa ofishin ba da umurni na sojojinta a Afirka a karkashin tutar "yaki da ta'addanci", to, za a tsunduma kasashen Afirka cikin barazanar ta'addanci. (Lubabatu)