

Yau na je dutsen Helan da ke yammacin birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia domin kallon zane-zanen da ke kan duwatsu, wadanda aka yi daga shekaru 10000 zuwa shekaru 1000 da suka gabata. A kan duwatsun da tsawonsu ya kai kilomita 250, an yi zane-zane fiye da dubu goma da ke bayyana zaman rayuwar dan Adam na zamanin jahilci, kamar kiwon dabbobi da raye-raye da yake-yake da yin addu'o'i da dai saurasu.
Wani kwararre ya bayyana cewa, a kan kira wadannan zane-zane da ke kan duwatsu da suna "fossil na al'adun gargajiya na dan Adam na zamanin jahilci", da kuma "tarihin 'yan kabilu makiyaya ta hanyar zane-zane".

Haka kuma zane-zanen da ke kan duwatsu sun bayyana al'adun gargajiya na mutanen da ke zamanin jahilci wajen ba da gaskiya ga halittu da totem da kakani-kakaninsu, kuma su muhimman shaidu wajen nazarin tarihin dan Adam da na addini da na al'adun gargajiya na zamanin jahilci na kasar Sin.

An bayyana cewa, yanzu zane-zanen da ke kan dutsen Helan suna neman shiga jerin kayayyakin tarihi na al'adun gargajiya na duniya. Haka kuma ana tsara shirin kare wadannan zane-zane domin dimbin mutane za su iya samun damar kallon al'adun gargajiya na dan Adam na zamanin jahilci.
|