Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 18:47:10    
Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta tana neman sabuwar hanyar tabbatar da ba da ilmi cikin adalci

cri
Makarantar midil ta Liu Panshan wata makaranta ce da gwamnatin birnin Yinchuan na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta kafa domin dalibai masu fama da talauci musamman. Wannan kuma makaranta ce da gwamnatin jihar Ningxia ta kafa lokacin da take neman hanyar ba da ilmi cikin adalci.

An kafa makarantar midil ta Liu Panshan ne a shekara ta 2004. Gwamnatin wurin ta kebe ta kudi, kuma ba ta karba kudin makaranta da na kwana na dalibai masu fama da talauci na gundummomi 9 na jihar. A waje daya kuma, ta samar wa kowane dalibi kudin Sin yuan dubu 1 a kowace shekara domin ba da tallafi ga zaman rayuwarsu. Ya zuwa yanzu, dalibai kusan dubu 3 da suka zo daga gundumomi 9 na jihar sun ci jarabawa suna karatu a cikin makarantar. Daga cikinsu, yawan dalibai masu bin addinin Musulunci ya kai kashi 40 cikin kashi dari, kuma yawan dalibai wadanda suka zo daga kauyuka ya kai kashi 80 cikin kashi dari.

Mr. Cai Guoying, direktan hukumar ba da ilmi ta jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta yana ganin cewa, gwamnati ta zuba kudaden gina wannan makaranta, kuma ta ba da ilmi ga nagartattun dalibai masu fama da talauci ba tare da karbar kudi ba domin gwamnatin wurin tana fatan za a iya samar wa dalibai masu fama da talauci damar samun ilmi cikin adalci.

"A da, mun dauki matakai da yawa, alal misali, kaurar da mutane da samarwa mutane masu fama da talauci tallafin neman bunkasuwa. Mun daidaita wasu matsaloli ta irin wadannan hanyoyi, amma idan ana son daidaita su gaba daya, dole ne a kyautata ingancin mutane da na al'umma. Wannan hanya ce ta ainihi."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta kuma ba da tallafin ba da ilmi ga yankuna masu fama da talauci, musamman ga yunkunan da kananan kabilu suke da zama. Yanzu, bisa sabon shirin ba da tallafin ilmi, gwamnatin kasar Sin tana samar da kudin Renminbi yuan biliyan 50 a kowace shekara, wato ta riga ta ba da tallafi ga dalibai miliyan 20. Madam Zhang Xiu, mataimakin direktan ofishin kula da harkokin kawar da talauci na jihar Ningxia ya ce, "ilmi ainihin maganin talauci ne. Mutane za su iya neman aikin yi ko kafa kamfanoni da masana'antu da kansu, kuma za su iya samun cigaba da yin gasa da sauran mutane cikin adalci bayan da suka samu ilmi."

A shekarar bara, Ma Sheng ta ci jarrabawar shiga makarantar midil ta Liu Panshan. Dukkan iyalansa suna fama da talauci sosai. Sabo da haka, yana farin ciki sosai domin ya ci jarrabawar shiga wannan makaranta. "A cikin makarantar da na yi karatu a da, ko malamai ko injunan ba da ilmi ba su da inganci, kuma babu injunan ba da ilmi na zamani. Amma a wannan makaranta, ana da dukkan injunnan ba da ilmi na zamani da muke bukata. Malamai ma sun kware sosai wajen ba da ilmi, kuma suna kula da zaman rayuwarmu kwarai."

Yanzu, wannan makarantar midil ta Liu Panshan na daya daga cikin makarantun midil 10 da suka fi kyau a jihar Ningxia. A shekarar bara, dalibai 604 na wannan makaranta sun zauna jarrabawar neman shiga jami'o'i da kwalejoji, dalibai 414 daga cikinsu sun ci jarrabawar shiga jami'o'i da kwalejoji. A shekarar da muke ciki, dalibai 1008 sun zauna jarrabawar neman shiga jami'o'in da kwalejoji, dalibai 745 daga cikinsu sun samu nasara. Wang Yanning wadda take karatu a aji na uku tana cike da imani ta gaya wa wakiliyarmu cewa, "Saboda garina yana da nisa da babban birane. Yanzu makarantar ta ba mu wata kyakkyawar damar yin karatu. Ina fatan zan iya koyon ilmin kasuwanci a Beijing. Ina fatan zan iya yin amfani da ilmin da na koya wajen raya garina." (Sanusi Chen)

Muna fatan za ku iya ba da sharhinku a kasa