Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 15:38:21    
Kasashen Turkey da Iran na hadin kansu a fannin makamashi don biya wa juna bukatu

cri

Ran 20 ga wata, a birnin Ankara, hedkwatar kasar Turkey, kasashen Turkey da Iran sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar hadin gwiwa game da samar da wutar lantarki a tsakaninsu. Wannan yarjejeniya ta biyu ce da kasashen biyu suka cim ma a fannin makamashi tun bayan watan Yuli na bana. Manazarta suna ganin cewa, ko da yake kasar Amurka za ta kakaba wa kasar Iran sabon takunkumi, amma duk da haka kasashen Turkey da Iran suna nacewa ga yin hadin gwiwarsu a fannin makamashi, wannan ya nuna a zahiri cewa, kasashen nan biyu suna yin haka ne don biya wa juna bukatu.

A karkashin yarjejeniyar nan, kasashen biyu za su zuba jari cikin hadin gwiwarsu don gina tasoshin samar da wutar lantarki masu aiki da makamashi biyu da tasoshin samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa da dama a kasar Iran, da kuma wata tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashi a kasar Turkey. A gun bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Parviz Fattah, ministan makamashi na kasar Iran ya bayyana cewa, ko da yake yarjejeniyar ta bakanta ran wasu kasashe, amma Iran da Turkey kasshe ne masu mulkin kai, sun daddale yarjejeniyar bisa manufar samun nasara tare.

A ganin manazarta, cikin fuskantar adawa mai zafin da kasar Amurka ke yi, a zahiri, kasashen biyu sun yi la'akari da abubuwa da yawa, suna ta inganta hadin gwiwarsu a fannin makamashi.

Na daya, kasar Iran wata babbar kasa ce mai albarkar makamashi a duniya. Yawan gurbataccen man fetur da gas da take samu ya kasance cikin sahun gaba a duniya. Amma kasar Turkey tana karancin makamashi kwarai. Yawan man fetur da gas da take shigowa daga kasashen waje don biya bukatunta ya wuce kashi 90 cikin dari. Ko da yake kasar ta yi iyaka da kasar Iraki mai albarkar man fetur sosai, amma saboda halin tsaron da ake ciki a kasar Iraki yana ta tabarbarewa a kwana a tashi, shi yasa ba mai yiwuwa ba ne, Turkey da Iran za su hada gwiwarsu a fannin makamashi. Banban da haka a ganin kasar Turkey, yin hadin gwiwa a tsakaninta da Iran yana da muhimmanci sosai. Don ta kasar Iran, yin hadin gwiwa a tsakanita da kasar Turkey zai rage hasarar da take yi daga wajen takunkunin tattalin arziki da gamayyar kasa da kasa ke kakaba mata. Bisa bukatun da kasashen biyu ke yi wa juna, yawan kudin da suka samu daga cinikinsu ya kai dalar Amurka biliyan 7 a shekarun nan da suka wuce, kuma an kyautata zaton cewa, yawan nan zai kai dala biliyan 10 a karshen shekarar nan. Ko shakka babu, hadin gwiwarsu a fannin makamashi yana taka muhimmiyar rawa wajen hakaba harkokin cinikayya a tsakaninsu cikin sauri.

Na biyu, kasashen biyu suna yin haka ne cikin la'akari da harkokin siyasa. A ganin kasar Iran, idan ta kusanci kasar Turkey, wadda ke ma'amala da kasashen yammaci musamman kasar Amurka, to, za a iya rage matsin da gamayyar kasa da kasa ke yi mata a wasu fannoni a halin yanzu.

Don ta kasar Turkey, ita za ta sami kyakkyawan sakamako wajen yin hadin kanta da kasar Iran a fannin makamashi. Amma manazarta suna ganin cewa, ya zuwa yanzu, akwai wasu abubuwan da ke kawo tasiri ga hadin kansu a fannin makamashi. Alal misali, Ross Wilson, jakadan kasar Amurka a Turkey ya nuna cewa, idan kasar Turkey ta soke yarjejeniyar hadin gwiwa kan gas a tsakaninta da kasar Iran, gwamnatin kasar Amurka za ta nuna cikakken goyon bayanta ga aikin raya makamashin da kasar Turkey ke yi a kasar Iraki da tsakiyar Asiya. Yanzu, kasar Turkey tana taka tsantsan a kan wannan shawara.

Ban da wannan kuma, majalisar wakilai ta kasar Amurka ta kafa dokar kakabawa kasar Iran takunkumi da karfi a kwanakin baya, za ta kakabawa kamfanonin kasashen waje takunkumi wadanda yawan jarin da suka zuba wa Iran jari a fannin man fetur da gas ya wuce dalar Amurka miliyan 20. A bayyane, yayin da Turkey ta fara aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa kan man fetur da gas a tsakanin kaashen Turkey da Iran, za a kakaba mata takunkumi. Sabo da haka za a kara lura cewa, ko kasar Turkey za ta canja manufarta ko a'a. (Halilu)