Masu sauraro,kwanakin baya ba da dadewa ba,aka soma gasar zagaye na farko a shiyyar Asiya don tace kungiyoyin da za su shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Afirka ta kudu a shekarar 2010,a gun gasar zagaye na farko,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Myama da 7:0.A cikin shirinmu na yau,za mu yi muku bayani kan wannan.
Ran 21 ga watan Oktoba da dare,a cibiyar wasan motsa jiki ta Fushan dake kudancin kasar Sin,masu sha`awar wasan kwallon kafa sun yi ihu da babbar murya,dalilin da ya sa haka shi ne domin kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Myama da 7:0.Wannan shi ne kokari a karo na tara da kungiyar kasar Sin ta yi domin shiga gasar karshe ta gasar cin kofin duniya,wato kafin wannan,kungiyar kasar Sin ta taba shiga gasar zagaye na farko don tace kungiyoyin da za su shiga gasar cin kofin duniya sau takwas,wadda a ciki,ta taba samun iznin shiga gasar karshe ta gasar cin kofin duniya da aka shirya a kasar Korea ta kudu da kasar Japan a shekarar 2002.Amma a shekarar 2006,ba ta shiga gasar karshe ta gasar cin kofin duniya ta kasar Jamus ba.Kuma a gun gasar cin kofin Asiya da aka yi a yanayin zafi na bana,kungiyar kasar Sin ba ta cim ma burinta na shiga kungiyoyi hudu na gaba ba.Wannan ya bata ran masu sha`awar wasan kwallon kafa na kasar Sin sosai da sosai.
Don daga matsayin kungiyar kasar Sin,kungiyar kula da wasan kwallon kafa ta kasar ta sake kafa kungiyar malaman koyar da wasa ta kasar Sin.A watan Satumba na bana,aka gayyaci shahararren malamin koyar da wasa daga kasar Serbia Vladimir Petrovic Pizon da ya zama malamin koyar da wasa mai zartaswa na kungiyar kasar Sin.A karkashin jagorancinsa,kungiyar samari wadanda shekarunsu na haihuwa ba su kai 21 ba na kasar Serbia ta taba samun zama na biyu a gun gasar cin kofin samarin Turai ta shekarar 2002,kuma daga shekarar 2004 zuwa shekarar 2006,Vladimir ya taba zama malamin koyarwa na kungiyar Shide ta Dalian ta kasar Sin,a karkashin jagorancinsa,kungiyar Shide ta zama zakara a shekarar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta shekarar 2005.
Bayan da Vladimir ya zama babban malamin koyarwa na kasar Sin,aikinsa na farko shi ne yin takara da kungiyar kasar Myama domin shiga gasar zagaye na farko tsakanin kananan kungiyoyi ta gasar cin kofin duniya ta kasar Afirka ta kudu ta shekarar 2010.
Game da halin da `yan wasan kasar Sin ke ciki,babban malamin kasar Sin Vladimir ya bayyana cewa, ``Yan wasa sun riga sun gane cewa,dole ne su yi iyakacin kokari domin samun sakamako mai kyau,yanzu dai,suna fatan matsayin wasan kwallon kafa na kasar Sin zai dada daguwa bisa kokarin da suke yi.`
A cikin atisayen da suke yi,a kullum Vladimir yana koyar musu fasahohin da ya samu,wato dole ne su mai da hankali kan hadin gwiwa tsakaninsu.A gun gasar dake tsakaninta da kungiyar kasar Myama,kungiyar kasar Sin ta jefa kwallo cikin raga sau bakwai,kyakkyawan bugu da suka yi ta sa masu sha`awar wasan kwallon kafa su yi ihu da babbar murya,kuma ana iya cewa,kungiyar kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara.Amma,Vladimir bai gamsu da wannan ba,ya ce :`Ko shakka babu,`yan wasa sun sanya matukar kokari,amma ba su yi amfani da damar shiga kwallo dake gabansu sosai ba,kamata ya yi su ci gaba da yin atisaye.`
Lallai kamata ya yi `yan wasan kwallon kafa na kasar Sin su ci gaba da yin kokari,amma nasarar da suka samu ta sa kaimi gare su,yanzu `yan wasan kasar Sin suna cike da imani.`Dan wasa wanda ya jefa kwallo daya a cikin raga a gun gasar dake tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Myama Liu Jian ya ce: `Wannan gasa ita ce ta farko da muka yi domin shiga gasar cin kofin duniya ta Afirka ta kudu,kuma daga wannan,ana iya ganin ci gaban da muka samu,ni ma ina fatan za ku ci gaba da nuna mana goyon baya kamar yadda kuka yi a da.` (Jamila Zhou)
|