Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 08:15:06    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (14/11-20/11)

cri

Ran 14 ga wata,kwamitin shirya gasar wasannin Olimpic ta Beijing ya sanar da salon lambar yabo ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008.An sa dutsen jade mai siffar zobe a gefen kowace lambar yabo,sa`annan kuma aka buga tambarin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008.A daya gefen daban kuwa,an buga tambarin kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya da sunan wasanni,Ban da wannan kuma an rubuta kalmomin `gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta shekarar 2008` da rubutun sinanci da turanci da kuma na rubutun makaho.

Ran 17 ga wata,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan karate a karo na tara wadda aka shafe kwanaki shida ana yinta a birnin Beijing na kasar Sin.A gun gasar da aka shirya,`yan wasan da suka zo daga kasashe daban daban sun yi takara domin neman samun lambobin zinariya da yawansu ya kai 40,kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya guda 18 daga cikinsu,wato yawan lambobin zinariya da ta samu sun fi yawa.Za a yi zama na goma na gasar nan a birnin Toronto na kasar Canada a shekarar 2009.

Ran 18 ga wata,aka yi gasar cin kofin duniya ta wasan Judo ta duniya ta shekarar 2007 a birnin Beijing na kasar Sin,a gun gasar maza,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Faransa,ta samu zama na uku tare da kungiyar kasar Rasha.Wannan shi ne maki mafi kyau da kungiyar `yan wasan judo ta kasar Sin ta samu a cikin babbar gasa ta duniya.A gun gasar karshe kuma,kungiyar kasar Japan ta lashe kungiyar kasar Brazil ta samu zama ta farko,kungiyar kasar Brazil ta zama lambatu.

Ran 17 ga wata,aka rufe babban taron yaki da magani mai sa kuzari ta duniya wanda aka shafe kwanaki uku ana yinsa a birnin Madrid na kasar Spain,a gun wannan babban taro,aka zartas da `ka`idar yaki da magani mai sa kuzari` da aka gyara,kuma za ta fara aiki a hukunce daga watan Janairu na shekarar 2009.Abu mafi bambanci dake tsakanin sabuwar ka`ida da ka`ida ta da shi ne aka tanada cewa,za a hana `dan wasa wanda ya sha magani mai sa kuzari a karo na farko da ya shiga gasa ta tsawon shekaru 4,amma a da,shekaru 2 ne kawai.

Ran 16 ga wata,aka gama gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon raga ta mata a kasar Japan,kungiyar kasar Italiya ta lashe kungiyar kasar Amurka ta zama zakara,wannan shi ne karo na farko da kungiyar kasar Italiya ta samu zama ta farko ta gasar cin kofin duniya. (Jamila Zhou)