Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-20 19:14:31    
Wen Jiabao ya bayyana manufofin bude kofa da na amincewa da juna da kasar Sin take dauka

cri

A ran 19 ga wata da yamma, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao wanda ke yin ziyara a kasar Singapore ya bayar da wani jawabi mai lakabi haka "bin manufar bude kofa ga kasashen waje da amincewa da juna kawai, kasar Sin za ta samu cigaba da karfi" a jami'ar kasar Singapore. A cikin jawabinsa, Mr. Wen ya jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje, kuma za ta kara mai da hankali kan yadda za a daidaita matsalolin da aka samu lokacin da ake aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje. Jawabinsa ya jawo hankulan masu sauraro na bangarori daban-daban na kasar Singapore.

A cikin nasa jawabi, Wen Jiabao ya hada tarihi da halin da ake ciki yanzu, kuma ya yi amfani da kididdiga da abubuwan gaskiya masu dimbin yawa lokacin da yake bayyana yadda kasar Sin take aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje na moriyar juna daga dukkan fannoni a cikin dogon lokaci mai zuwa. Wen ya ce, "Bude kofa ga kasashen waje babbar manufa ce da kasar Sin ke bi, amma ba manufa ce da aka dauka domin wani dan lokaci kawai ba. Ba ma kawai muna bude kofarmu ga kasashe masu arziki ba, har ma muna bude kofa ga kasashe masu tasowa. Kuma ba ma kawai muna bude kofa ga kasashen waje a fannin tattalin arziki ba, har ma muna bude kofa ga kasashen waje a fannonin kimiyya da fasaha da ilmi da al'adu da dai sauransu. A waje daya kuma, ba ma kawai wannan manufa tana amfanawa kasar Sin ba, har ma tana amfanawa cigaban sauran kasashen duniya. Kasar Sin ta shigar da jari da fasahohi na kasashen waje, wannan zai raya karfin kawo albarka na kasar Sin. Sannan kasashen waje za su iya samun moriya da kasuwanni a kasar Sin."

Wen Jiabao ya kuma bayyana cewa, bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufofin bude kofa ga kasashen waje. Mr. Wen ya kuma bayyana yadda za a daidaita matsalolin da aka samu lokacin da ake aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje. Mr. Wen ya ce, "Muna fatan za a yi ciniki cikin 'yanci, kuma ba mu amince da ra'ayin kafa katangar cinikin waje ba. Kuma za mu cigaba da kyautata tsarin cinikin kudin Renminbi. A waje daya, muna mai da hankalinmu sosai kan ingancin kayayyaki da na abinci. Za mu sauke nauyin da ke bisa wuyanmu ga dukkan masu sayen kayayyaki kirar kasar Sin. Bugu da kari kuma, za mu ci gaba da kuma karfafa yin hadin gwiwa da kasashen waje kan kokarin kiyaye ikon mallakar fasaha."

Mr. Tsai wanda ya saurari jawabin da Wen Jiabao ya bayar, ya tambayi firayin minista Wen cewa, "Yanzu ana fadin cewa, kasar Sin masana'anta ce ta duk duniya. Ko yaya kasar Sin za ta samu daidaito kan batutuwan neman cigaba da kiyaye muhalli?" Game da wannan tambaya, Mr. Wen ya ba da amsa cewa, "Masana'antun kire-kire na kasar Sin suna samun cigaba cikin sauri. Amma ba a iya kiransu masana'antun kasashen duniya ba. Saboda a cikin masana'antun kire-kire, kayayyaki masu mallakar fasahohin zamani ba su yi yawa ba. Ba ma kawai jama'ar kasar Sin suna amfani da kayayyaki kirar kasar Sin ba, har ma jama'ar sauran kasashen duniya suna amfani da su. Game da batun gurbata muhalli da ka ambata, abun gaskiya ne da yake kasancewa a kasar Sin. Lokacin da kasar Sin take samun cigaba cikin sauri, dole ne mu mai da hankalinmu kan wannan batu. Yanzu zan iya gaya maka cewa, tun daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar da muke ciki, yawan makamashin da muka yi amfani da shi domin samun kowane kudin samar da kayayyaki na kasa ya ragu da kashi 1.8 cikin kashi dari. Yawan abubuwa masu gurbata muhallin da aka fitar ya riga ya ragu da kashi 0.28 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Yanzu lokaci ne na canja halin da muke ciki a kasar Sin lokacin da take samun cigaba."

Ba ma kawai Mr. Lee Kuan Yew, tsohon firayin ministan kasar Singapore yana cike da imani ga makomar kasar Sin ba, har ma ya amince da cewa cigaban da kasar Sin ta samu zai amfanawa kasashen da suke makwabtaka da ita. "Ko da yake an dan samu gargada wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, amma muna da imani ga kasar Sin da ta zama wata kasa mai karfi a fannin tattalin arziki a duk duniya." (Sanusi Chen)