Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-19 20:30:13    
Gwamnatin kasar Sin ta bawa matasa kyaututtukan fatan alheri na FUWA na wasannin Olympics na Beijing

cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Hsinhua na kasar Sin ya bayar,an ce ana nan ana shirya bukukuwan taimakon jama'a tare da nufin sada zumunci a tsakanin jama'a da shirya wasannin Olympics cikin yanayin jituwa a larduna da jihohi sama da 29 na kasar Sin. Tun da aka fara bikin matasa sama da dubu dari daga iyalai masu fama da talauci sun samu irin kyaututtukan fatan alheri na FUWA.

Fuwa abubuwan kawo alheri ne na wasannin Olympics na Beijing a shekara ta 2008.Yawansu ya kai biyar. Sifoffinsu kamar kifi,dabar Panda da dabar antelope na Tibet da tsuntsun Swallow da wutar torcila na wasannin Olympic.

Kwamitin shirya wasannin Olympics na shekara ta 2008 na birnin Beijing da ma'aikatar ilimi ta kasar Sin sun hada kansu sun tsara wani shirin <fadakar da 'yan makarantun firamare da sakandare kan wasannin Olympics na shekara ta 2008 na birnin Beijing> duk domin wayarwa jama'a kai kan wasannin Olympics.Bawa kyautar kawo alheri Fuwa wani kashi ne na shirin nan.Bisa labarin da aka samu,an ce kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing zai saye cikakkun kyautocin Fuwa dubu 290 zai rarraba su ga larduna da jihohi 29 na kasar Sin wato kowansu ya samu cikakkun kyaututtukan Fuwa guda dubu dari.(Ali)