Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-19 20:24:18    
An rufe taron koli na dandalin tattaunawa kan dinkuwar dukkan kasar Sin gaba daya

cri

A ran 18 ga wata an rufe taron koli na dandalin tattaunawa kan batun sa kaimi ga dinkuwar dukkan kasar Sin gaba daya a birnin Washington na kasar Amurka. Wakilan Sinawa wadanda suke da zama a wurare daban-daban sun yi taro tare, inda suka tattauna halin da ake ciki a gabobi biyu na mashigin teku na Taiwan da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka da batun tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.

A cikin nasa jawabin da ya yi a gun bikin kaddamar da taron, Zhou Wenzhong, jakadan kasar Sin da ke kasar Amurka ya yaba wa dukkan Sinawa wadanda suke da zama a ketare domin sun taka muhimmiyar rawa ba tare da kasala ba wajen kokarin raya huldar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin ruwan sanyi da sa kaimi ga dinkuwar dukkan kasar Sin gaba daya cikin lumana. Ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan matsayin bin maufar Sin daya tak, da ciyar da huldar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan gaba cikin ruwan sanyi da hada kan dukkan 'yan uwanmu na Taiwan cikin sahihanci domin bayar da kokari tare wajen farfadowar al'ummar dukkan kasar Sin. A waje daya, Zhou ya ce, gwamnatin kasar Sin tana yaki da dukkan ayyukan neman 'yancin kan Taiwan da ake yi ta kowace hanya, ko shakka babu za ta kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan dukkan kasar Sin. Ya ce, "Yanzu masu neman 'yancin kan Taiwan suna gaggauta ayyukan kawo wa kasar Sin baraka. Suna lalata kokarin raya huldar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan cikin ruwan sanyi. 'Yan uwa na gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan sun yi yaki, kuma hana ayyukan neman 'yancin kan Taiwan, musamman matakan neman 'yancin kan Taiwan bisa doka, ciki har da kada kuri'a domin neman shigar da Taiwan cikin majalisar dinkin duniya da hukumar Chen Shuibian ta Taiwan suke yi, nauyi mafi muhimmanci kuma mafi gaggawa da ke bisa wuyansu."

Lokacin da yake batu kan huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, Zhou Wenzhong ya bayyana cewa, batun Taiwan batu ne mafi muhimmanci kuma mafi jawo hankulan mutane a cikin huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Ya ce, "Mun yaba wa gwamnatin kasar Amurka domin sau da dama kuma a fili ne take bayyana matsayin kin amincewa da matakin 'kada kuri'a domin neman shigar da Taiwan cikin majalisar dinkin duniya' da hukumar Taiwan ke yi. Bangaren kasar Sin yana fatan bangaren kasar Amurka zai gane hadari da barazana da sakamako mafi tsanani na ayyukan neman 'yancin kan Taiwan da hukumar Chen Shuibian ke yi, kuma zai ci gaba da cika alkawarinta na bin manufar Sin daya tak a duk fadin duniya, da kin amincewa da neman 'yancin kan Taiwan."

Mr. Zhang Manxin, wakilin kungiyar sa kaimi kan dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana ya bayyana cewa, "Dukkan batutuwan da suke da nasaba da ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunan kasar, dole ne dukkan Sinawan da suke hada da Sinawa miliyan 50 da suke da zama a ketare sun tsai da kuduri tare. Ko tsirarrun masu neman 'yancin kan Taiwan su canja hanyarsu, har ma su yi amfani da ra'ayin wasu mutane, a kan wannan ka'idar Sin daya tak a duniya, dukkan Sinawa, ciki har da Sinawan da suke da zama a ketare ba su cimma tudun dafawa ba."

Mr. Zhang Wujiu, wanda ya kai shekaru 84 da haihuwa, kuma yanzu yake da zama a kasar Brazil, shugaba ne na kungiyar nahiyar kudancin Amurka ta sa kaimi kan dinkuwar duk kasar Sin gaba daya ya bar kasar Sin a shekarar 1949, kuma ya taba yin zama a Taiwan har na tsawon shekaru 30. Sakamakon haka, ya fi mai da hankalinsa kan bunkasuwar Taiwan. Dattijo Zhang ya ce, "Na riga na kai shekaru 84 da haihuwa. Ina da imani cewa, lokacin da nake rayuwa a nan duniya, za a iya dinkuwar dukkan kasar Sin gaba daya." (Sanusi Chen)