
Bayan da muka ratsa tabki ta kananan kwale-kwale, wata hamada ta fito a gaban idanunmu. Wannan shi ne karo na farko da na ga hamada, na ji mamaki sosai da kyaun ganinta. Rakumi dabba ce da aka fi nuna kauna gare shi a cikin hamada, kuma a kan kiranshi "kwale-kwale da ke cikin hamada". Na hau wani rakumi na isa kolin dutsen rairayi da tsayinsa ya kai kusan mita dari, lalle hamadar da ba a iya ganin bakinta ba ta yi kamar wani tekun rairayi mai launin zinari. Daga baya kuma na kwanta a cikin hamada na sha hasken rana, na ji dadi kwarai da gaske.(Kande) 1 2
|