Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-16 15:47:01    
Kasuwar tsofin kayayyaki mai suna Panjiayuan da ke birnin Beijing

cri
Cikin shahararren wuraren shakatawa da ke birnin Beijing, ya kasance da wata kasuwar tsofin kayayyaki mai suna Panjiayuan. A ko wane karshen mako, masu yawon shakatawa na gida da na waje su kan je kasuwar don su zabi kayayyakin fasaha irin na gargajiya da suke so.

Gail Cohen wadda ta zo daga kasar Amurka ita ce daya daga cikin wadannan masu yawon shakatawa. Ta ce, 'A cikin littafin jagorar ziyarar yawon shakatawa, an ce, idan an yi yawon shakatawa a Beijing, kada a manta da wurin. Dazu nan, ina kallon wani zanen da aka yi kan bawon itace, gaskiya ne yana da ban sha'awa.'

Abin da ya janyo hankulan mutane kan kasuwar Panjiayuan shi ne, za a iya sayen kayayyakin fasaha na kasar Sin masu inganci da araha a nan. Ban da wannan kuma, a cikin kasuwar, mai yiwuwa ne, za a sayi kayayyakin fasaha masu daraja da kudin kadan. Ga misali, wani mutum ya kashe kudin Renminbi yuan 15 ya sayi wani takobi, daga baya ya sayar da shi yuan dubu 150. Wannan abu ne da kan faru a wurin.

Cui Xinwei, mai kula da kasuwan nan ya gaya wa maneman labaru cewa, abin da ya sa irin wannan abu ya faru shi ne, kayayyakin da ake sayarwa a cikin kasuwar dukansu 'yan kasuwa suka tattara su ne a wurare dabam daban na kasar Sin, cikin wadannan 'yan kasuwa wasu suna da ilimi kan tsofin kayayyaki, wasu kuma ba a wayar musu da kai ba, shi ne ya ba mutum damar samun garabasa. Mista Cui ya ce, ko wace rana akwai masu tattara tsofin kayayyaki da yawa wadanda ke yawo a tsakanin shaguna, ke duduba kayayyaki da tabaron likita.

'Wadannan kwararru kan tattara tsofin kayayyaki su kan zo da sassafe. Sabo da yawon da suka yi a cikin kasuwar nan ne, suka kara iliminsu wajen tattara kayayyaki, kuma abubuwan da suka tara sun karu.'

An kafa kasuwar Panjiayuan ne a shekaru 13 da suka wuce. Da farko, wasu mazunan da ke kurkusa da wurin su kan sayar da tsofin kayayyakin gidansu a can. Daga baya gwamnati ta yi garanbawul kan kasuwar, ta kara girmanta. Yanzu ko da yake ana kiranta kasuwar tsofin kayayyaki, amma a hakika kuma za ka iya samun ko wane iri kayayyakin fasaha na kasar Sin a can, kamarsu kayayyakin gida na gargajiya, da tsofaffin littattafai, da dutse mai daraja, da kayan fadi-ka-mutu, da tsofin kudade, da tufafin al'umomi, da dai sauran makamantansu. Fadin kasuwar ya kai muraba'in mita dubu 50, ya kasance da shaguna fiye da 4000 a ciki.

Yanzu an riga an mai da kasuwar Panjiayuan daya daga cikin wuraren shakatawa na Beijing. Kuma an mayar da ziyarar kasuwar Panjiayuan, da hawan babbar ganuwa, da cin gasashen agwagwa na Beijing, da kuma ziyarar fadar sarki su 4 a jeri daya, don su zama abubuwa guda 4 da ya kamata 'yan yawon shakatawa su yi a birnin Beijing.

Yanzu cikin masu sayen abubuwa da ke kasuwar, 'yan yawon shakatawa daga kasashen waje suna da yawa. Don haka an kafa allunan alamar jagora da yawa, wadanda ake rubutu a kansu da Sinanci da Turanci, ta yadda za a amfana wa masu sayen kayayyaki baki. Ban da wannan kuma, a karshen mako wato ran Asabar da Lahadi, a cikin kasuwar, masu ba da jagora wadanda ke iya Turanci su kan ba da taimako ga masu sayen kaya na kasashen waje. Kang Qian, daya daga cikinsu ya ce,

'Da na gamu da baki yayin da nake zagayawa a cikin kasuwar, na kan gaya musu zan iya ba da taimako a kyauta. Da suka gaya mini abin da suke so, sai in kai su inda ya dace.'