Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-16 10:16:22    
Za a kayyade yawan bukukuwan nune-nune da za a shirya a Beijing kafin karshen gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta shekarar 2008

cri

A ran 15 ga wata, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, bisa "ka'idojjin shirya bukukuwan nune-nune da ke shafar dukkan kasar Sin ko irin na kasa da kasa a yankin Beijing kafin, ko a lokacin da ake yin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta shekarar 2008" da ma'aikatar ta bayar a kwanan baya, za ta kayyade ba da izinin shirya irin wadannan bukukuwan nune-nunen kafin ko a lokacin da ake yin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta shekarar 2008.

Bisa ka'idojin da aka tsara, a tsakanin ran 1 ga watan Augusta zuwa ran 23 ga watan Satumba na shekarar 2008, ba za a ba da izinin shirya bukukuwan da ba su da nasaba da wasannin motsa jiki na Olympics ba. Haka kuma a tsakanin ran 30 ga watan Afrilu zuwa ran 31 ga watan Yuli na shekarar 2008, za a kayyade ba da izinin shirya bukukuwan da ke shafar duk kasar Sin ko irin na kasa da kasa. A tsakanin ran 30 ga watan Afrilu zuwa ran 23 ga watan Satumba na shekarar 2008, idan ana da shirin shirya bukukuwan da suke da nasaba da gasar wasannin motsa jiki ta Beijing ta shekarar 2008, ya kamata hukumar da abin ya shafa ta gabatar da takardar neman izinin shirya bukukuwa daga wajen kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Beijing. Sannan za a tsai da kuduri bisa ra'ayin kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Beijing ta shekarar 2008 da ka'idojin da abin ya shafa. (Sanusi Chen)