Ran 10 ga wata, a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, an bude taron wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin a karo na 8. A cikin taron wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu na wannan karo mai tsawon kwanaki 8, an fito da manyan gasanni guda 15 da kuma wasu 149 wadanda aka yi ne ba tare da samun lambar yabo ba. Yanzu 'yan wasa fiye da 6300 na kungiyoyin wakilai 34 na dukan kasar Sin suna karawa da juna a Guangzhou. Taron wasannin da ake yi a wannan karo ya fi girma a tarihin taron wasannin motsa jiki na gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin.
Ran 12 ga wata, an kaddamar da cibiyar yaki da amfani da magani mai sa kuzari ta kasar Sin, wadda za ta yi bincike kan misalai 4500 ta fuskar magani mai sa kuzari a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa. Yawan ma'aikata masu bincike zai kai 150, a ciki har da kwararru na ketare 20. Bayan taron wasannin Olympic na shekara mai zuwa, cibiyar za ta ba da hidimar yau da kullum a fannin yin bincike kan ko an yi amfani da magani mai sa kuzari ko a'a. Mataimakin shugaban hukumar harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin malam Duan Shijie ya bayyana cewa, kafuwar cibiyar yaki da amfani da magani mai sa kuzari ta kasar Sin wani babban ci gaba ne daban da gwamnatin Sin ta samu a fannin inganta ayyukan yaki da amfani da magani mai sa kuzari.
Ran 7 ga wata, wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, babban filin wasa na taron wasannin Olympic na Beijing, wato Bird's nest, wanda aka kan kira shi hakan, zai bakunci gasa a karo na farko a watan Afirilu na shekara mai zuwa. An labarta cewa, babban filin wasa na kasar Sin wato Bird's nest zai kawo karshen ginawa a karshen watan Maris a shekara mai zuwa. Tun daga ran 18 zuwa ran 19 ga watan Afirilu na shekara mai zuwa, za a yi gasar kalubale ta wasan iya tafiya da sauri ta kasa da kasa a wannan filin wasa, wadda ke matsayin wani bangare na gasar 'GoodLuck Beijing', kuma yana kasancewa gasa ta farko da za a yi a wannan filin wasa.
Ran 9 ga wata, Li Qing, shugaban sashen ba da hidima domin gasanni na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, ko da yake abincin kasar Sin mai dadin ci ya shahara sosai a ko ina a duniya, amma duk da haka, abinci irin na kasashen yamma zai sami rinjaye a cikin dukkan abincin da za a samar a gun taron wasannin Olympic na Beijing na shekara mai zuwa. Wannan jami'i ya kara da cewa, yanzu ana nan ana inganta da kyautata takardar sunayen abinci na taron wasannin Olympic na Beijing a karon karshe. Abincin kasashen yamma zai kai kashi 70 cikin kashi dari bisa dukkan abincin da za a samar a gun taron wasannin Olympic na Beijing, wato ke nan, abincin kasar Sin da sauran irin abinci zai kai kashi 30 cikin kashi dari. An riga an tabbatar da wasu masana'antun mafi karfi, wadanda suke ba da kyakkyawar hidima, kuma suna gudanar da ayyukansu bisa tsauraran ma'auni, a matsayin 'yan kasuwa masu samar da abinci a lokacin taron wasannin Olymic na Beijing.(Tasallah)
|