A ganin dimbin mutanen kasashen waje, birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin wani birni ne da suke iya raya ayyukansu da kuma jin dadin zaman rayukansu. Yau na yi intabiyu tare da Stephen Newenhisen, wani dan Amurka da ke gudanar da wani karamin dakin sayar da Pizza na kasar Amurka a birnin Yinchuan.
Mr. Stephen ya zo daga jihar Ohio ta kasar Amurka, kuma ya gama karatunsa daga jami'ar Regis ta kasar, kafin ya zo kasar Sin, ya gudanar da wani kamfanin gine-gine. Ya san birnin Yinchuan daga wata jarida, sai nan da nan birnin ya jawo hankalinsa sosai. Shi ya sa a shekara ta 2006, shi da matarsa da kuma yaransa sun zo birnin Yinchuan. Mr. Stephen ya gaya mini cewa, idan ana ganin cewa, biranen Beijing da Shanghai sun riga sun samu bunkasuwa sosai, to binrin Yinchuan ya fara samun bunkasuwa ba da jimawa ba. Sabo da haka a idonsa, ya yi sa'a ya iya samun wannan zarafi mai kyau wajen raya aikinsa.
Bayan da ya yi bincike kan sha'anin abinci na birnin Yinchuan, ya gano cewa, 'yan birnin suna iya karbar abincin kasashen waje cikin sauki, shi ya sa ya tsai da kudurin bude wani dakin sayar da pizza na kasar Amurka.
Mr. Stephen yana ganin cewa, idan ana son gudanar da wani dakin cin abinci kamar yadda ya kamata, to dole ne ya iya tabbatar da ingancin abinci da kyakkyawan aikin ba da hidima da kuma muhallin cin abinci mai kyau.
Sabo da wadannan ka'idojin gudanar da dakin cin abinci da Mr. Stephen ya tsara sun yi daidai, shi ya sa ya jawo hankulan mutanen da suka zo daga kasashen Korea ta Kudu da Japan da Amurka da Canada da Phillipine da da Jamus sosai. Dalilin da ya sa wadannan baki su kan je wurin shi ne sabo da ba kawai suna iya jin dadin cin abinci ba, har ma suna jin kamar suna gida.
Muna fatan za ku iya ba da sharhinku a kasa
|