Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-13 18:27:43    
Kasar Sin tana kokarin tabbatar da yawan haihuwa da ake yi a kauyuka a matsayi mafi kankanta

cri
Yau kasar Sin ta soma wani taron aiki game da yawan mutane da aikin aiwatar da manufar haihuwa bisa tsari a kauyuka a birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan. A gun taron, Mr. Hua Jianming, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki matakan tabbatar da yawan haihuwa da ake yi a kauyuka a matsayi mafi kankanta ta hanyoyin kyautata shirin ba da tallafin kudi ga gidajen da suke haihuwa bisa tsari da kara sa ido, da ba da hidima kan mutanen karkara 'yan cirani,

Tun daga shekaru 70 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta soma aiwatar da manufar haihuwa bisa tsari a duk fadin kasar. Ya zuwa yanzu jimlar mutanen da ba a haife su ba ta kai miliyan dari 4. Saboda haka, an tabbatar da kafa hulda mai jituwa a tsakanin dan Adam da tattalin arziki da zaman al'umma da muhalli da albarkatun halittu. Amma har yanzu kasar Sin tana fuskantar matsala mai tsanani kan batun yawan mutanenta, musamman a kauyuka inda yawan mutanensu ya kai kashi 63 cikin kashi dari bisa na dukkan yawan mutanen kasar Sin.

A gun taron kwanaki 2, Mr. Hua Jianming, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ce, kasar Sin za ta dinka kyautata shirin ba da tallafin kudi ga mutane wadanda suke bin manufar haihuwa bisa tsari a kauyuka. Mr. Hua ya ce, "Irin wannan shirin ba da tallafin kudi ga mutane wadanda suke bin manufar haihuwa bisa tsari hanya ce ta ba da jagoranci ga jama'a da su kayyade yin haihuwa da kansu. Saboda haka, wannan sabuwar hanya ce da aka kirkira wajen aiwatar da manufar haihuwa bisa tsari, kuma dawaumammiyar manufa ce ga kokarin tabbatar da yawan haihuwa da ake yi yake kan matsayi mafi kankanta. Ya kamata wurare daban daban su ci gaba da kyautata wannan hanya."

An bayyana cewa, tun daga shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta bayar da manufa cewa, ta soma samar wa gidajen kauyuka da suke haihuwa sau daya ko sau biyu kawai tallafin kudin da yawansa ba zai yi kasa da kudin Renminbi yuan dari 6 a kowace shekara. Sannan gwamnatin kasar Sin ta kara yawan tallafin kudin da take bai wa irin wadannan gidaje. Alal misali, yanzu gwamnatin kasar Sin tana bai wa kowane manomi ko makiyayi na yankunan yammacin kasar da yake bin manufar haihuwa bisa tsari kudin Renminbi yuan dubu 3 a kowace shekara, kuma tana taimakon shi kan yadda zai iya amfani da wannan kudi kan kokarin kawo albarka da fama da talauci. Idan yaran irin wadannan gidaje sun mutu ko sun zama nakasassu, tabbas ne gwamnatin kasar Sin ta ba su tallafin kudi bisa ma'aunin da aka tsara. Tun daga shekarar 2004 zuwa yanzu, yawan irin wadannan tallafin kudin da gwamnatin kasar Sin ta samar ya riga ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 4.5. A shekarar da muke ciki kawai, yawan manoman da suka samu moriya daga wannan shiri ya kai miliyan 2 da dubu dari 3 da 30.

A waje daya kuma, a gun taron, Mr. Zhang Weiqing, shugaban kwamitin kula da harkokin yawan mutane da manufar haihuwa bisa tsari na kasar Sin ya bayyana cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta hada da manufofin moriyar jama'a da manufofin moriyar manoma da manufar samar da tallafin kudi ga gidajen da suke aiwatar da manufar haihuwa bisa tsari domin kara samar wa irin wadannan gidaje manufofin moriyarsu wajen neman aikin yi da kiwon lafiya da ba da ilmi. Mr. Zhang ya ce, "Lokacin da gwamnatin kasar Sin take aiwatar da ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta da shirin ba da tabbacin kiwon lafiya a kauyuka, tana sa gidajen da suke bin manufar haihuwa bisa tsari a gaban sauran gidaje. Tana fatan jama'a wadanda suke bin manufar haihuwa bisa tsari za su iya samu moriya mafi yawa."

Bugu da kari kuma, lokacin da gwamnatin kasar Sin take aiwatar da shirin ba da tallafin kudi a kauyuka, tana kuma kara sa ido da ba da hidima ga manoma 'yan cirani da yawansu ya yi yawa kan batun haihuwa. (Sanusi Chen)