Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-13 17:15:45    
Birnin Dali a kudancin kasar Sin

cri

Masu yawon shakatawa na gida da waje suna sha'awar wadannan abubuwan birnin Dali ainun da ba safai a kan iya samunsu a sauran wurare ba. Masu yawon shakatawa wadanda ke zuwa birnin Dali su kan yi yawa. Akwai wani titi da ake kira Huguo cikin Sinanci a birnin Dali. Tsawon titin nan ya kai misalin mita 1000. An shimfida wannan titi ne da duwatsu masu launin tsanwa. An kafa dakunan cin abinci irin na Turawa da dakunan shan kofi da sauransu masu kayatarwa a bakin titin nan. A nan ne, masu yawon shakatawa da yawa da suka fito daga kasashe daban daban su kan ci abinci, da shan ruwan kofi da hutawa. Haka zakila wasu baki 'yan kasashen waje sun dade suna zaune a cikin gidaje da suka yi haya a bakin hanyar nan, sabili da haka ana kiran titin nan da wani suna daban na wai "titin baki 'yan kasashen waje".

Bayan da Malama Geraldine Laurendeau, 'yar yawon shakatawa ta kasar Canada ta yi yawon shakatawa a birnin Dali, ta bayyana cewa, "birnin Dali ya bayyana mini kyakkyawar alama. Karin harshe na Sinanci da ake magana a birnin nan ya sha banban da na sauran wurare na kasar Sin. Ina sha'awarsa ainun, kuma na iya magana da shi kalma-kalma. Abin da ya sa na koyi karin harshen nan shi ne domin kara fahimtar al'adun birnin da kyau. A ganina, 'yan birnin Dali da sauran jama'ar lardin Yunnan suna nuna wa baki aminci sosai. Birnin Dali wuri ne mai ni'ima kwarai. Kuma na kan ji dadi da yin hira da su." (Halilu)


1 2