Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-12 15:22:40    
Babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan ta jihar Ningxia

cri

Yankunan da ke kan duwatsu da ke kudancin jihar Ningxia su yankuna ne da ke fama da talauci mai tsanani a kasar Sin, inda ba a iya samun malamai masu nagarta da kyawawan makarantu, sabo da haka dimbin yara ba su da damar shiga manyan makarantun sakandare. A shekara ta 2002, gwamnatin jihar Ningxia ta tsai da kudurin kafa babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan a birnin Yinchuan, hedkwatar jihar domin daukar yaran da ke yankunan da ke kudancin jihar, ta yadda za a iya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar jihar, da inganta hadin gwiwa tsakanin kabilu daban daban na kasar Sin, da gaggauta bunkasuwar aikin koyarwa na yankunan da ke kan duwatsu a kudancin jihar, da kuma kyautata ingancin mutane masu fama da talauci.

Gwamnatin jihar Ningxia ita ce ta samar da dukkan kudaden karatu da na wuraren kwana ga 'yan makaranta masu fama da talauci, ban da wannan kuma ta samar da kudin Sin wato Yuan 1000 ga ko wane dan makaranta ko 'yar makaranta da suka zo daga kauyuka a ko wace shekara. Ta haka, 'yan makaranta masu nagarta da ke yankunan da ke kan duwatsu suna iya shiga birni da kuma samun ilmi kamar yadda yaran da ke birane ke yi ba tare da biyan ko kwabo ba.


1 2