Masana'antar FEZA wata masana'anta ce ta sarrafa ma'addinan cobalt da tagulla da kasar Sin ta zuba jari a kai a kasar Congo(Kinshasa). A da masana'antar FEZA tana dogara da kone katako domin bushe danyun kayayyaki. Ko da yake ta sami izni daga hukumomin wurin da abin ya shafa, amma saboda ta yi la'akari da cewa, wannan aiki ya kan kawo wa gandun daji barna, shi ya sa ma'aikatan fasaha na masana'antar FEZA suka sha yin dabara, a karshe dai sun fito da wata hanya mai kyau, wato sun yi kwaskwarima kan injunan samarwa domin jigilar hayakin da suke fitowa a lokacin sarrafa cobalt da tagulla zuwa murhun bushe kayayyaki ta bututu, ta haka, masana'antar FEZA ta magance kone katako, haka kuma, ta yi amfani da hayakin da aka yi watsi da su domin bushe danyun kayayyaki.
A halin yanzu, karin masana'antun kasar Sin sun je kasashen Afirka domin samun bunkasuwa, sa'an nan kuma, yawan masana'antun Sin da suka yi la'akari da kiyaye muhalli a ayyukan kawo albarka, kamar masana'antar FEZA take, yana ta karuwa sannu a hankali.
Don kawar da abubuwan da ke gurbata muhalli, wadanda kuma aka samu daga wajen ayyukan kawo albarka, kamfanin NFC Africa Mining Public Limited Company da ke karkashin shugabancin kamfanin China Nonferrous Metal Mining Co. Ltd wato CNMC ya tsara shirin daidaita abubuwan gurbata muhalli, inda ya mai da hankali kan kiyaye muhalli da riba da kuma raya zaman al'ummar kasa na wurin tare cikin daidai wa daida.
Ga misali, kamfanin ya kafa masana'antar tsabtace ruwa. Bayan da ya tsabtace ruwa, ya sake yin amfani da wani kashi na ruwan, ya samar wa masana'antun da ke makwabtaka da shi wani kashi daban, sauran kuwa, ya samar da shi ga masana'antun samar da ruwan sha na wurin, inda bayan da suka sake tsabtace ruwan, su kan samar da shi ga mazaunan wurin domin zaman rayuwa, ta haka, an inganta aikin sake amfani da ruwa.
Ayyukan kiyaye muhalli da masana'antun kasar Sin suke yi sun sami amincewa daga gwamnatocin wurin da kuma babban yabo daga mazaunan wurin. Wani jami'in kamfanin NFC Africa Mining Public Limited Company ya ce, a shekarun baya, kudaden da kamfaninsa ya kashe wajen sayen ire-iren takardun samun iznin fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sun yi ta raguwa a ko wace shekara, wannan shi ne sakamakon da kamfaninsa ya samu bisa aiwatar da shirin kiyaye muhalli.
An yi karin bayanin cewa, a shekarun nan da suka wuce, sauye-sauyen yanayi ya zama wata matsala a gaban dukkan kasashen duniya. Haka kuma, sakamakon bincike ya nuna cewa, kasashen Afirka ba su da isasshen karfi wajen daidaita wannan matsala. A cikin irin wannan hali ne yawancin kasashen Afirka suka inganta tunanin kiyaye muhalli, a sa'i daya kuma, suna alla-alla wajen samun tallafi daga kasashen duniya a fannonin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da kuma tinkarar sauye-sauyen yanayi.
Ko da yake kasashen Afirka sun yi kokarin kiyaye muhalli, amma duk da haka, yawancinsu suna da karancin fasaha da injuna da kwararru. Yanzu wasu masana'antun kiyaye muhalli na kasar Sin sun riga sun fara yin hadin gwiwa tare da hukumomin kasashen Afirka da abin ya shafa.
A watan Yuli na wannan shekara, wani kamfanin sumunti na kasar Faransa da ke kasar Senegal ya fara aiki da tsare-tsare 2 na tattara kura cikin jaka, wadanda kamfanin Henan SINOMA Enviromental Proection Co. Ltd da ke karkashin shugabancin kamfanin China National Materials Group Corporation wato SINOMA ya yi kwaskwarima da kuma hada su. Ta haka, an kwantar da kura, wadda ta sha damun birnin Dakar saboda gurbata muhalli. Wannan aikin da Sinawa suka yi ya sami matukar yabo daga 'yan kasar Senegal.
Game da sauye-sauyen yanayi, karin masana'antu sun gano cewa, kiyaye muhalli wani muhimmin bangare ne a fannin gudanar da harkokin masana'antu ta hanyar zamani. Ayyukan gaskiya da masana'antun kasar Sin suka yi a harkokin kiyaye muhalli a Afirka sun shaida cewa, masana'antun kasar Sin suna ta samun ci gaba a fannonin kyautata tunani da hanyoyin tafiyar da ayyukansu a Afirka.(Tasallah)
|