---- Bayan kwamitin duddubawa da bincike da ke hade da manyan sufaye na addinin Buddha na Tibet ya yi jarrabawa sosai, dalibai 11 da suka yi karatu domin samun wannan babban digiri a karo na 3 na kolejin koyon addinin Buddha na Tibet sun samu digirin da ake kira "Tho ram pa", wato digiri mafi girma a wannan addini.
Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu labari daga wajen bikin ba da digirin da aka yi a nan birnin Beijing cewa, , domin gudanar da manufar bin addinan kasar Sin cikin 'yanci, da sa kaimi ga tallafa wa manyan sufaye a addinin Buddha na Tibet, kuma bisa yardar da aka samu daga wajen gwamnatin kasar Sin, an fara gudanar da tsarin ba da wannan babban digirin master na addinin Buddha na Tebet da ake kira "Tho ram pa" daga shekarar 2004, kolejin koyon addinin Tibet na kasar Sin ce take daukar nauyin gudanar da wannan tsarin karatu. Yawan mutanen da suka kasance da wannan babban digiri ya kai 33 a kasar Sin.
---- A ran 22 ga wata, bisa gayyatar hukumar M.D.D. da ke kasar Sin ta yi mata ne, kungiyar makadan gargajiya ta kabilar Naxi wadda ta zo daga bakin kogin Li na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin ta nuna wasanni a babban dakin kide-kide na Zhongshan da ke nan birnin Beijing musamman domin murnar zagayowar "ranar M.D.D." ta 62.
Shugaban kungiyar makadan gargajiya ta kabilar Naxi, kuma mai yin jagorancin kungiyar ya bayyana cewa, kide-kiden gargajiya sun zama sakamako ne da aka samu ta hanyar harhada al'adun kabilu da yawa na kasar Sin, kuma yana fatan wannan fasahar kide-kiden gargajiya za ta iya sanar da duk duniya cewa, ya kasance da madogarai da yawa a duniya, ya kamata al'adu iri daban-daban na duniya su samu bunkasuwa cikin jituwa.
Sakon kayatarwa da aka bayar daga M.D.D. ya ce, "wannan wasan da za a yi zai zama wani bikin da ya fi jawo hankulan mutane daga cikin bukukuwan da aka shirya domin murnar ranar M.D.D. ta wannan shekara, wasu jami'o'in hukumomin majalisar da ke kasar Sin, da jakadun kasashen waje da ke kasar Sin da kuma jami'o'in kasar Sin da yawa za su halarci wannan shagalin kide-kide.
An ce, halin musamman mafi garma na kide-kiden gargajiya na kabilar Naxi shi ne irin wadannan kide-kide ya hada kide-kide da kayayyakin kide-kiden tarihi masu tsawon shekaru dubu daruruwa, kuma makada masu yin kide-kide yawancinsu tsofaffi ne wadanda suka ba shekaru 70 baya, sabo da haka ana kiran irin wadannan kide-kide da sunan "daraja mai rai".
|