Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 16:14:30    
Masallaci na Nanguan na birnin Yinchuan

cri

Dukkan 'yan kabilar Hui suna bin addinin Musulunci, kuma yawansu ya kai sulusi na dukkan yawan jihar Ningxia ta kasar Sin, shi ya sa ana iya ganin abubuwan da ke nuna al'adun musulunci a ko ina a jihar Ningxia, ciki har da masallatai masu yawa.

Yau na je masallaci na Nanguan da ke birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia domin yin intabiyu tare da shugaban kwamitin kula da harkokin masallacin Alhaji Muhanmode Younusi.

Masallacin Nanguan yana daya daga cikin masallatai mafi girma na jihar Ningxia, yana da benaye biyu. Babban dakin yin salla yana bene na sama, inda musulmai kusan 1000 ke iya yin salla tare, kuma wurin wanka da dakunan limamai da kuma azuzuwa suna bene na kasa. Ana iya samun manya da kananan dakuna fiye da dari a masallacin.

Masallatai na kasar Sin suna da halin musamman nasu, wato suna kafa kwamitocin kula da harkokin masallatan domin tattara asusun kudaden addini da kuma gudanar da shi, da kula da harkokin gyara masallatai, da shiyar harkokin addinin musulunci iri daban daban, da kuma neman mayan limamai.

Alhaji Muhanmode Younusi, shugaban kwamitin kula da harkokin masallacin Nanguan wani tsoho ne da ke da kwarjini sosai. Ko da yake shekarunsa ya kai 80 da haihuwa, amma yana da lafiya kwarai da gaske. Ya gaya mini cewa, musulmai na kasar Sin har na duk duniya suna son zaman lafiya, ba su son yaki ko kadan. Haka kuma a karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, musulmai na kasar Sin suna zama tare da sauran 'yan kabilu na kasar cikin lumana sosai.