Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 15:36:44    
Yankin Hongkong na share fagen daukar wutar yula ta taron wasannin Olympics na Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, a cikin shirinmu na yau dai, za mu dan gutsura muku wani bayani kan yankin Hongkong na kasar Sin, inda za a gudanar da gasar sukuwar dawaki ta taron wasannin Olympics na Beijing. In ba ku manta ba, tuni a watan Mayu na shekarar da muke ciki, kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa sun kaddamar da hanyar mika wutar yula ta taron wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008 a fadin duk duniya. Yankin Hongkong yana daya daga cikin zanguna, inda za a gudanar da harkar mika wutar yula. To, yaya ne yankin Hongkong yake shirin karbar wutar yula?

Bisa shirin da aka tsara na hanyar da za a bi wajen bai wa juna wutar yula a fadin duk duniya, an ce, za a kai wutar yula mai tsarki ta taron wasannin Olympics a ran 2 ga watan Mayu na shekara mai zuwa. Da zarar aka bayar da labarin, sai bangarori daban-daban na yankin Hongkong suka yi hasashen cewa, lallai wannan ya kasance daya daga cikin matsaloli mafi muhimmanci a tarihin wasannin motsa jiki na Hongkong. Aminai masu sauraro, ko kuna sane da cewa, ya kasance da tazarar sama da kilo-mita 2,000 tsakanin yankin Hongkong da birnin Beijing. Saboda haka ne, wasu mutane suka bayyana shakkunsu cewa ko za a iya kirkiro wani irin kyakkyawan mhalli na taron wasannin Olympics yayin da ake gudanar da gasar sukuwar dawaki a nan yankin. Hakan ya janyo hankulan mazauna yankin. Amma kudurin gudanar da bikin mika wutar yula ta taron wasannin Olympics na Beijing a yankin Hongkong da aka tsaida, babu tantama ya samar da kyakkyawar dama ga yankin wajen yayata hasashen wasannin Olympics da kuma jawo mazauna yankin masu tarin yawa. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na Hongkong na kasar Sin Mr. Timothy Fok ya fada wa wakilinmu cewa: " Abu mafi muhimmanci shi ne yayata hasashen wasannin Olympics yayin da ake gudanar da harkokin wasannin bisa ingantaccen matsayi mafi koli. Za mu yi namijin kokari wajen samo hanyoyi iri daban-daban don fadakar da akasarin mazauna yankin ba wai nagartattun 'yan wasa kawai ba don su shiga wasannin Olympics".

Sanin kowa ne, ya kamata a yi aiki da kyau wajen kaddamar da hanyar mika wutar yula idan ana so a kirkiro wani kyakkyawan muhalli na taron wasannin Olympics. Mr. Pang Chong, babban sakataren kungiyar masu aikin sa kai ta kwamitin wasannin Olympics na Hongkong ya yi farin ciki matuka da waiwayen yadda aka mika wutar yula ta taron wasannin Olympics na Tokyo na shekarar 1964 a yankin Hongkong. Ya furta cewa: " A lokacin, da zarar wani jirgin sama ya sauka a filin saukar jiragen sama na Qide sai nan take aka fitar da wutar yula mai tsarki daga cikin jirgin. Sa'annan aka yi amfani da wani jirgin ruwa don daukar wutar yula zuwa babban dakin daruwar jama'a domin gwada ta ga mazauna yankin. Da dare ya yi, sai aka mika ta zuwa wani daki mai agogon garu, wanda ya kasance wani wuri ne dake da ma'anar tarihi domin gwada ta ga jama'a. Daga baya dai, aka sake dawo wa filin jiragen sama na Qide daga Zirin Jiu Long".

Jama'a masu sauraro, a matsayin wani mamban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, kwamitin wasannin Olympics na Hongkong na kasar Sin na da ikon zaben mutane masu rike da wutar yula cikin cin gashin kai. Yanzu, ya rigaya ya tabbatar da zaben shahararren mawaki mai suna Jackie Chang da kuma wata sannanniyar 'yar wasan kwallon badminton mai suna Yip Pei-yin don su zama masu rike da wutar yula ta taron wasannin Olympics na Beijing. Game da wannan dai, Mr. Pang Chang ya fadi cewa: " Wani muhimmin labari shi ne, shekara mai zuwa, lokaci ne na wuce shekaru goma da aka dawo da yankin Hongkong cikin hannun kasar mahaifa. Saboda haka, za mu yi amfani da wannan kyakkyawar damar mika wutar yula a yankin wajen bayyana kyakkyawar fuskarsa, wanda ya fi kyau bisa shekarar 1997 da kuma 1998". . ( Sani Wang )