Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 15:39:04    
Jihar Ningxia ta kasar Sin

cri

Bayan haka,akwai kuma malam Babangida Adamu da ya rubuto mana cewa, shin da gaske akwai Musulmai masu dunbun yawa a jihar Ningxia, tare kuma da Yakubu Mohammed Rigasa daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya da dai sauransu wadanda suka turo mana ra'ayoyinsu, amma mun kasa karanto su duka, sabo da karancin lokaci. Amma mun riga mun sanar da Kande a kan ra'ayoyinku, kuma za ta yi kokarin kawo muku abubuwan da kuke so ku kara ilmi dangane da jihar Ningxia. Amma yanzu, sai bari mu dan bayyana muku yadda wannan jiha ta Ningxia ta kasance daga wasu manyan fannoni, don ku sami takairaccen ilmi a kanta.

Jihar Ningxia mai zaman kanta ta kabilar Hui na daya daga cikin jihohi guda biyar masu zaman kansu na kananan kabilun kasar Sin, kuma ta kafu ne a watan Oktoba na shekarar 1958. Fadin jihar Ningxia ya kai muraba'in kilomita dubu 66.4, kuma yawan mutanenta ya kai kusan miliyan 6, daga cikinsu, yawan 'yan kabilar Hui, wadanda ke bin musulunci, ya kai miliyan 1 da dubu 990, wadanda suka dau kashi daya daga cikin uku na mutanen jihar, tare kuma da kashi daya daga cikin biyar na dukan 'yan kabilar Hui a kasar Sin, sabo da haka, jihar Ningxia ta zama mazauni mafi girma na 'yan kabilar Hui a kasar Sin. Sakamakon dimbin 'yan kabilar Hui musulmi da ke zaune a jihar Ningxia, Ningxia ta kuma zama jiha ta musulmi a kasar Sin, har ma gaba daya akwai masallatai da suka wuce 3,000 a jihar, wadanda suka samar da irin yanayi na musulunci sosai.

Ko da yake jihar Ningxia ba ta da fadi, amma duk da haka, tana da arzikin albarkatun kasa iri iri, har ma tana daya daga cikin manyan shiyyoyi hudu na ban ruwa da kuma manyan yankuna guda 12 wadanda ke fitowa da hatsi a kasar Sin. A can shiyyar, ayyukan masana'antar abinci da sarrafa fata da nama da madara da kuma giyar inabi duka su ne suka fi shahara a jihar Ningxia. Bayan haka, Ningxia tana kuma shahara da dimbin arzikin kwal da take da su, wadanda ke da inganci kwarai da gaske, kuma ya zuwa yanzu, yawan kwal da aka gano a jihar Ningxia, ya riga ya kai ton biliyan 31, wanda ya zo na shida a kasar Sin. A jihar Ningxia, akwai wani shahararren filin mai da iskar gas, wanda har ya kai matsayin duniya, kuma yawan man fetur da iskar gas da ke filin ya kai cubic mita biliyan 700, wanda ya samar da kyakkaywar makoma ga Ningxia wajen bunkasa masana'antun man fetur da gas.

Bayan haka, jihar Ningxia ta kuma kasance wuri mai kyau a wajen yawon shakatawa. Kasancewar jihar Ningxia a hanyar gargajiya ta siliki, Ningxia tana da dadadden tarihi. Tun tuni a shekarar 1038, an kafa daular Xixia a wurin. A jihar, akwai dimbin wuraren tarihi masu ban mamaki da sha'awa. Ban da wuraren tarihi, akwai kuma wurare masu ni'ima na halitta. Masu sauraro, idan wata rana kun sami damar zuwa jihar Ningxia, ba shakka, jihar Ningxia za ta burge ku da daddaden tarihinta da irin al'adunta na musamman da kuma ni'imtattun wurarenta.

Masu sauraro, mun dai kawo muku takaitaccen bayani a kan jihar Ningxia ta kasar Sin, watakila akwai masu sauraronmu da ke cewa, kai, dan takaitaccen bayani bai ishe mu ba, to, ba damuwa, sai ku bi sawon wakiliyarmu Kande wadda ke yin ziyara a jihar, don ta kawo muku cikakkun labarai game da jihar. Kada kuma ku manta, mun kebe wani fili na musamman dangane da ziyarar Kande a jihar Ningxia a shafinmu na internet, inda kuke iya samun bayani dangane da jihar, kuma adireshinmu na internet shi ne hausa.cri.cn. (Lubabatu)


1 2