Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-08 17:09:42    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (7)

cri

---An samu wata frofesa a wata jami'a da ta rera waka da taka rawa a cikin ajin makaranta.A cikin jami'ar kudu maso yammanci dake a birnin Chongqing na kasar Sin akwai wata frofesa da ta rera waka da taka rawa a yayin da take koyarwa.Batun nan ya jawo hankulan daliban jami'ar nan.

Sunan frefesa shi ne Li Dawu tana da shekaru 58 da haihuwa ta fara rera wakoki ne yayin da take koyar da darusa kan adabi duk domin kara gishiri a ciki saboda a ganin daliban darusan ba su da abin sha'awa a ciki.Yau shekaru 25 ke nan da ta rera wakoki a jami'a a matsayin malamar koyarwa sabili da hak dakunan ajinta kullum suna cike da wakoki da dariya.

---Ana so a sake nada suna ga dabbobi biyu na Panda.Ana so a sake nada suna ga dabbobi biyu a wurin shakatawan dake da dabbobi na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin,shi ya sa hukumar kula da wurin ta kaddamar da wata gasar nada suna tare da bayar da tsaraba ga mai nasara.Duk wanda zai iya ba da sunaye masu dacewa ga dabbobi biyu na Panda kafin ran 25 ga watan Oktoba zai samu kudin kyauta na kudin Sin Yuan dubu biyar.Dabbobin Panda biyu an haife su ne a shekara ta 1995 da shekara ta 1994 a lardin Sichuan na kasar Sin,a wancan lokaci ana nada daya suna Xinxing dayan kuwa Di Di.Wurin kula da dabbobi yana fatan a sake nada suna ga Xin Xing wadda ta fi ci abinci mai yawa da Di di wadda ba ta so zaman lafiya.

----Wani dan ci rani yana jin dadin zama a wurin kiwo dabbobi.Mr Zhang Laicheng,dan ci rani ne da ya zo daga wurin Guannan na lardin Jiangsu na kasar Sin,ya isa birnin Chongqing a shekara ta 1992.Shi bai taba yin tsammanin yin zama wurin kiwo dabbobi ba.Lokacin da ya isa wurin,an dauke shi a matsayin mai kula da furanni,amma shi ma ya yi aiki da yawa a gidan kiwo dabbobin Panda,daga bisani ya zama mai kula da dabbobin panda a shekara ta 1996.Yanzu ya kusa zama gwani wajen kula da dabbobin panda bayan da ya yi aiki sama da shekaru sha daya da suka shige.Ya yi dan suna a fannin nan.Yayin da yake renon dabbobi,ya iya kwantar da hankalinsu.

----Wata mata mai tunanin soyayya ta fadi daga itace.Wata mata mai tunanin soyayya ta fadi daga kan itace yayin da take cire furannin ice har ma an kai mata asibiti domin ba da magani sabo da kashinta ya karye.Sunan matar Qian Yu mai shekaru 60 da haihuwa,mijinta Tian Fan dukkansu su kan dauki furannin itacen kamar wani abin tunaniya da ya fadakar da zamansu kafin shekaru arba'in da suka gabata.A farkon wannan wata sun koma gidan mahaifinta inda ta girma,tare da nufin tunanin zamaninsu na fara soyayya,sai ta hau ice ta cire furanni,daga baya ta fadi kasa aka kai mata asibiti.

----Iyayen yarinya sun ci tara saboda suka mari abokiyar yarinya.A yankin mulkin musamman na Hongkong na kasar Sin,an sami wani miji da matarsa wadanda suka mari abokiyar diyarsu da suke tsammanin ita 'yar madigo ce,daga baya an ci musu tarar kudin dalar Hongkong 2500.Yayin da iyayen yarinya sun ga 'yar madigo mai shekaru 13 da haihuwa,sai sun zarge ta,ita ma ta mayar da martani da zargi,da haka iyayen sun mari ta.An ce 'yar madigo ta kan shiga kayan maza,yayin da suka shiga yanar internet suna kiran sunan juna da "miji da mata".

----Gardamar iyali kan dukiyoyi.Wani mutum daga Hongkong ya bukaci wata hukuma da ta shiga tsakani kan gardama tsakaninsa da 'yanuwansa.Ya ce 'yanuwansa su kan dame shi yayin da yake neman a aiwatar da wasiyyar uwarsu.Mai gabatar da kara shi ne Mr Cheng.ya ce dangantaka dake tsakanin 'yanuwansa ta lalace bayan da ya samu kudin dalar Hongkong budu 74 bisa wasiyyar uwarsa wadda ta rasu a shekara ta 2000.Kafin uwarsa ta rasu ta sayar da dukiyoyinta ta samu kudin dalar Hongkong miliyan 9.3,ta rarraba wa 'yanuwansa daidai wa daida.Yayin da Mr Cheng ya bukaci wansa da ya bayyana dukiyoyin uwarsu gaba daya,ya shure shi.

----An kama masu caca da kudi a Hongkong..A makon jiya wasu 'yan sanda na Hongkong sun shiga wani dakin dake cikin hotel inda suka kama mutane goma da suka yi caca da kudi ciki har da mata guda uku.Kafin sun same su.'Yan sandan sun sami labarin cewa wani garken mutane sun yi hayar dakin hotel sim yi caca da kudi.Sai 'yan sanda sun sa fararen kaya sun buga kofar dakin,sun ce mun baci wasu abubuwa a cikin dakin,da suka bude kofar an kama su nan take.

---Wani mutum ya ajiye bindiga bayan da ya kuskura ya harbe karen wani makwabcinsa a ido.Wani mutum a Hongkong ya yi watsi da dabiarsa na rike da bindiga bayan da ya ci tara saboda ya kuskura ya harbe karen wani makwabcinsa a ido.Sunan mutumin nan shi ne Chan Yuen Lon,yana da shekaru 57 da haihuwa.Ya ce ya saye wannan bindiga na wasa domin yana sha'awarsa kwarai da gaske ya kan yi amfani da shi bayan lokacin aikinsa.Mr Chan ya ce ya yi gwajin bindiga ne a gida,ba zato ba tsammani ya harbe karen a ido.Ya ci tarar kudin dalar Hongkong dubu 15 haka kuma ya biya makwabcinsa da dalar Hongkong 5700.Ya gaya wa alkalai cewa ba zai yi amfani da bindiga ba,maimakon haka ya bukaci dansa da ya koya masa amfani da yanar internet.

---Wata mata ta kan yi karya.An samu wata mata a birnin Zhengzhou na lardin Henan wadda ta kan yi karya kan yawan shekarunta da sau nawa ta yi aure.Daga baya mijinta ya gabatar da ita a gaban kotu.Sunan mata shi ne Pan,tana da shekaru 47 da haihuwa amma ta ce tana da shekaru 37 kawai.Ta taba kashe aure sau biyu,amma ta ce sau daya kawai.Mijinta Yin nada shekaru 42 da ya gane matarsa ta cuce shi,sai ya gabatar da ita gaban kotu domin yin rabuwa da mata.