
Ina murna sosai sabo da na sani da wannan zarafi wajen yin mu'amala tare da ku masu karanta shafinmu na Internet. Daga yau zuwa ran 4 ga wata mai zuwa, zan gudanar da aiki a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai da ta kasar Sin, shi ya sa a ko wace rana, zan nuna muku wasu hotunan da na dauka, kuma zan rubuta wasu labarai game da abubuwan ban sha'awa da na ji kuma na gani a jihar.

Isowata a birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ke da wuya, sai birnin ya jawo hankalina nan da nan bisa kyaun ganinsa da kuma ci gabansa. Sanin kowa ne, yankunan da ke yammacin kasar Sin ba su fi na gabashin kasar ci gaba ba, shi ya sa kafin in zo jihar, ina ganin cewa, ko shakka babu, jihar tana a baya. Amma abubuwan da ke gaban idanuna sun canja ra'ayina wajen ci gaban jihar.

Ko da yake lokacin sanyi ya yi, amma ana iya ganin ciyayi da bishiyoyi masu yawa a ko ina a birnin Yinchuan. Idan dare ya yi kuma, birnin ya fi kyaun gani. Ana kunna fitilu a ko ina, birnin ya zama wani abin al'ajabi, kuma ka na iya jin irin albarkar da wannan birni ke da shi.
|