Yanzu a kasar Sin,an fara gudanar da wasan kwallon kwando na sana`a ba da dadewa ba,ana yin kokari wajen samun ribar kasuwanci.Ko shigowar NBA zai matsa lamba ga bunkasuwar wasan kwallon kwando ta kasar Sin?Game da wannan,Li Yuanwei ya bayyana cewa,lallai wasan kwallon kwando na kasar Sin yana fuskantar matsin lamba,amma yana iya mayar da martani kamar iznin dake gabansa,shi ya sa kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin ta yi maraba da NBA da ta shiga kasuwar kasar Sin,haka kuma za a ciyar da kasuwar wasan kwallon kwando ta kasar Sin gaba.Ya ce, `Muna yin hadin gwiwa da NBA,kuma muna yin kokari domin kara karfafa da kuma habaka kasuwar wasan kwallon kwando ta kasar Sin,kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin tana bude kofa domin yin maraba da hukumomi da kamfanoni na wasan kwallon kwando na kasarshen waje.`
Li Yuanwei yana ganin cewa,wasan kwallon kwando babban sha`ani ne,kuma kasuwar wasan kwallon kwando ita ma babbar kasuwa ce,idan ana so a kara karfafa da kuma habaka kasuwar nan,dole ne a bude kofa kuma a yi hadin gwiwa da hukumomin kasashen waje.Yanzu dai kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin tana yin shawarwari da NBA kan hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban daban,kuma tana yin kokari domin yin hadin gwiwa da sauran hukumomin da abin ya shafa,a karshe dai,za a sami ci gaba tare.Ya ce, `Abokin hadin gwiwa daya bai isa ba,muna fatan za mu yi hadin gwiwa da abokai da yawa,idan an ga damar amfanawa sha`anin wasan kwallon kwando na kasar Sin,za mu yi kokari.` ?Jamila Zhou) 1 2
|