Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-07 17:39:22    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (31/10-06/11)

cri

Ran 31 ga watan jiya,a gun babban taron 62 na majalisar dinkin duniya,gaba daya aka zartas da `kudurin tsagaita bude wuta domin wasannin Olimpic`,kasar Sin ta gabatar da wannan kuduri,kuma kasashen mambobin majalisar dinkin duniya da yawansu suka kai 186 sun daddale kudurin.Wannan shi ne karo na takwas da babban taron majalisar dinkin duniya ya dinga zartas da `kudurin tsagaita bude wuta domin wasannin Olimpic`.Shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing Liu Qi ya bayyana cewa,ba ma kawai `tsagaita bude wuta domin wasannin Olimpic` shi ne tunanin wasannin Olimpic ba,har ma shi ne fata daya na jama`ar kasashen duniya wadanda ke kishin zaman lafiya.Liu Qi ya kara da cewa,kirayin babban batun taron wasannin Olimpic na birnin Beijing shi ne `duniya daya,mafarki daya`,kuma muhimmin tunaninsa shi ne `tsabtattacen wasannin Olimpic da wasannin Olimpic masu kimiyya da fasaha da kuma al`adu`,dukkan wadannan sun nuna mana cewa,jama`ar kasar Sin da na kasashen duniya suna yin kokari domin neman samun zaman lafiya da bunkasuwa cikin lumana.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,a birnin New York na kasar Amurka,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogge ya karfafa cewa,za a daidaita matsalar gurbacen iska a gun taron wasannin Olimpic na birnin Beijing kamar yadda ya kamata.Rogge ya bayyana cewa,matakan da kasar Sin ta dauka suna da amfani sosai da sosai kuma cikin gaggawa,alal misali,an canja makamashin kamfanoni daga kwal zuwa gas,kuma an dasa miliyoyin bishiyoyi,ban da wannan kuma a gun taron wasannin Olimpic,za a rage mota wajen milliya daya.

Ran 3 ga wata ne,an kammala gasar cin kofin duniya na wasan dambe na duniya na shekarar 2007 a birnin Chicago na kasar Amurka,gaba daya an shirya gasa na aji 11,kungiyar kasar Sin ta samu lambar zinariya daya da lambobin tagulla 4,kuma ta samu izni bakwai na shiga taron wasannin Olimpic na Beijing.

Ran 4 ga wata,an kammala gasar koli wato premiership ta wasan kwallon badminton na kasar Faransa na shekarar 2007 a birnin Paris na kasar,a cikin gasar karshe da aka shirya a wannan rana,`yan wasan kasar Sin sun samu zakaru uku wato zakarar mata da zakaran gasa tsakanin mata biyu biyu da kuma zakaran gasa tsakanin maza biyu biyu. ?Jamila Zhou)