Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-05 20:27:03    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Bisa labarin da aka samu daga hukumar yanayin sama ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, an ce, daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, za a kafa tashoshin binciken yanayin sama 57 a muhimman wuraren noma da makiyayai na jihar domin ba da hidima ga aikin noma da kiwon dabbobi cikin yanayin mai kyau.

Bisa bayanin da wani jami'in da abin ya shafa na hukumar yanayin sama ta jihar Tibet ya bayar an ce, gina wadannan tashoshin binciken yanayin sama zai kyautata matsayin jihar Tibet wajen ba da hidima ga aikin noma da kiwon dabbobi a fannin yanayin sama, da kara karfin yaki da bala'o'in hallita a wannan fanni.

Jihar Tibet wata jiha ce da ta sha bala'o'i daban-daban sabo da mugun yanayi, kuma jiha ce inda akan yi sauye-sauyen yanayi da raunanan halittu masu rai. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sabo da yanayin duniya yana ta kara dumama, shi ya sa munanan yanayi iri daban-daban sukan auku a jihar Tibet wadanda suka haddasa babbar hasara da illa.

---- Ana kokarin tallafa wa lauyoyi 'yan kananan kabilu a jihar Xinjiang ta kabilar Uighur, wato jiha mafi fadi mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kananan kabilu ta kasar Sin, kuma za a rika ba da wannan tallafi ne ga kwararrun lauyoyi na kananan kabilu a duk lokacin da ya dace.

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yawan lauyoyi 'yan kananan kabilu na jihar Xinjiang ma yana ta karuwa ba tare da tsayawa ba. Ya zuwa watan Satumba na shekarar 2007, yawan lauyoyi 'yan kananan kabilu da ake da su a jihar Xinjing ya kai 380, wato ya kai kashi 17 cikin 100 bisa jimlar lauyoyin da ake da su a jihar. Jihar Xinjiang tana mai da muhimmanci wajen tallafa wa lauyoyi 'yan kananan kabilu, an zabi wasu lauyoyi daga jihar kuma an kawar da su zuwa sauran wurare masu sukuni na kasar Sin don su kara samun ilmi ta hanyar yin bincike, kuma akan gabatar musu da sabbin dokokin da aka buga cikin harshen kabilun Uighur, kuma an nuna babban goyon baya wajen kudin yin tallafin da kuma gabatar musu da bayanai.

---- Gwamnatoci daban-daban na jihar Tibet suna nan suna kara rubanya kokari wajen kiyaye kayayyakin tarihi na al'adun gargajiya na jihar, a wannan shekarar da muke ciki, jihar nan za ta shigar da wurare fiye da 60 cikin sunayen hukumomin kiyaye kayayyakin tarihi bisa matsayin jiha mai ikon tafiyar da harkokin kanta.

Shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, akwai arzikin albarkatun kayayyakin tarihi sosai a jihar Tibet, yawan ni'imtattun wuraren ban sha'awa na tarihi da aka yi rajista ya kai fiye da 2,330 a jihar.

Gwamnatin kasar Sin kullum tana mai da muhimmanci wajen kiyaye kayayyakin tarihi na jihar Tibet, sabo da haka jimlar kudin da gwamnatin kasa da ta jihar suka ware domin wannan aiki ya wuce kudin sin wato Yuan miliyan 700.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)