A ran biyu ga wata, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya tashi zuwa kasar Uzbekistan, inda ya fara ziyararsa a kasashe hudu na Turai da Asiya. A cikin gajerun kwanaki biyar ne, Mr.Wen Jiabao zai halarci taron firaministocin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai a karo na shida, kuma zai kai ziyarar aiki a kasashen Uzbekistan da Turkmenistan da Belarus da kuma Rasha, kuma zai halarci ganawar da za a yi a tsakanin firaministocin kasashen Sin da Rasha a karo na 12 da kuma bikin rufe "shekarar Sin" da ake yi a kasar Rasha. Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana wa manema labarai a kwanan baya cewa, wannan ziyarar da Mr.Wen Jiabao zai yi zai kara fahimtar juna a tsakanin Sin da kasashen hudu a fannin siyasa da kuma inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban, kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar da kuma duniya baki daya.
Birnin Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan, ya kasance zango na farko a wannan ziyarar da Mr.Wen Jiabao ke yi, kuma a wurin, zai halarci taron firaministoci a karo na shida na kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai. A cikin shekarar da ta gabata, kungiyar hadin kai ta Shanghai ta yi ta bunkasa kwarai da gaske, a watan Agusta na shekarar da muke ciki, kasashe mambobin kungiyar sun gudanar da taron koli a birnin Bishkek, har ma sun daddale "yarjejeniyar sada zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai", daga baya, sun kuma gudanar da atisayen soji na yaki da 'yan ta'adda cikin hadin gwiwa, wanda ya kasance irinsa mafi girma da kungiyar ta gudanar a tarihinta. A sa'i daya, mambobin kungiyar sun kuma cimma manyan nasarori a hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin ba da ilmi da al'adu da kiyaye muhalli da dai sauransu.
Mr.Li Hui, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin ya ce, a cikin irin wannan hali ne, gudanar da taron firaministoci na da muhimmiyar ma'ana a wajen inganta nasarorin da aka samu a gun taron koli na Bishkek da kuma inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar. Ya ce,"a gun taron firaministoci a wannan karo, Mr.Wen Jiabao da kuma firaministoci na sauran kasashe za su takaita nasarorin da aka samu a hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyar hadin kai ta Shanghai a fannonin tattalin arziki da al'adu, kuma za su yi nazari na musamman a kan yadda za a tabbatar da yarjejeniyar sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai da dai sauran yarjejeniyoyin da aka cimma a gun taron koli na Bishkek."
Game da ziyarar da Mr.Wen Jiabao zai kai wa kasashen Uzbekistan da Tukmenistan, Mr.Li Hui ya ce, yau shekaru 13 ke nan da firaministan kasar Sin ya sake kai ziyara a kasashen biyu, ga shi kuma a daidai lokacin cika shekaru 15 da Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da su, shi ya sa ziyarar na da ma'ana ta musamman, ya ce,"Uzbekistan da Turkmenistan muhimman kasashe ne guda biyu a tsakiyar Asiya, haka kuma makwabta ne masu aminci da kasar Sin. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, huldar da ke tsakanin Sin da Uzbekistan da kuma Turmenistan ta bunkasa yadda ya kamata, kuma an cimma manyan nasarori a hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban."
Shekarar da muke ciki ta kasance wata muhimmiyar shekara a tarihin huldar da ke tsakanin Sin da Rasha, kuma huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Rasha ta kai wani sabon matsayin. An ce, a lokacin ziyararsa a Rasha, Mr.Wen Jiabao zai gana da shugaba Putin na Rasha, kuma zai gana da sabon firaministan Rasha, Viktor Zubkov a karo na 12. Mr.Li Hui ya bayyana cewa,"A wannan ziyarar da zai kai wa Rasha, Mr.Wen Jiabao zai yi shawarwari tare da shugabannin Rasha cikin sahihanci a kan yadda za su tabbatar da daidaiton da suka cimma da kuma inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban tare kuma da tabbatar da bunkasuwar huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, sa'an nan, za su yi musanyar ra'ayoyi a kan manyan batutuwan da ke tsakanin bangarorin biyu da na duniya da kuma na shiyya shiyya."(Lubabatu)
|