Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-02 16:53:16    
An gudanar da tattalin arziki da kyau cikin watanni 9 na farkon wannan shekara

cri

A ran 2 ga wata a birnin Beijing, wani jami'in kwamitin bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin ya nuna cewa, a cikin watanni 9 na farkon wannan shekara, an gudanar da tattalin arziki da kyau, amma har ila yau, an samu karuwar sana'o'in da suke bata makamashi da yawa.

Mataimakin shugaban hukumar gudanar da tattalin arziki na kwamitin bunkasuwa da gyare-gyare ta kasar Sin, Zhu Hongren ya furta cewa, cikin watanni 9 na farkon bana, masana'antun kasar sun ci gaba da bunkasa da sauri kamar yadda suka yi a farkon rabin shekarar nan, yawan kudin da suka samu wajen sarrafa dukiyoyinsu ya karu fiye da kashi goma sha takwas cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, kuma saurin karuwarsu ya yi daidai da na farkon rabin shekarar bana. Ban da wannan kuma, yawan kayayyakin da wasu daga cikin sana'o'in da suka fi bata makamashi suka harhada, da wadanda suka fitar da su zuwa ketare sun sami raguwa. Dadin dadawa, manyan sana'o'in masana'antu 12 wato na narke karfe da samar da kayayyakin gine-gine da kera injuna da harhada maguguna da kuma na samar da lantarki da sauransu, sun cimma burin samun riba mai tsoka.(Lami)