Madam Meng Xiaoyan mai shekaru sama da talatin da haihuwa siririya ce wadda kuma takan yi murmushi yayin da take yin magana. Ita wata mai aikin shari'a ce kawai. Amma bambancin dake tsakaninta da sauran mutane shi ne tana mai sha'awar yin aikin hidimomi cikin son rai kuma ba tare da kasala ba. Madam Meng Xiaoyan ta zo ne daga jihar Guangxi na kasar Sin. Kuma ta soma aikin shari'a a shekarar 2004 bayan ta sauke karatu daga Jami'ar Beijing. Kuma tana daya daga cikin wadanda suka yi rajistan aikin sa kai domin taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008.
Kasancewar Madam Meng Xiaoyan a matsayin wata mai aikin sa kai tana da nasaba da halinta na kaunar mutane da yin hidimomi domin jama'a. Tuni a shekarar 1996 yayin da take karatu a cikin aji na biyu na kolejin koyon ilmin shari'a na Jami'ar Beijing, ta taba bai wa kananan yara na garinta kudin bonas da ta samu a karo na farko daga Jami'ar. A lokacin, akwai mutane da dama da ba su fahimce ta a game da wannan lamari ba. Amma Madam Meng Xiaoyan ta yi farin ciki da fadin cewa : ' Ina so in tallafa wa kananan yara na garinmu da kudin bonas da na samu a karo na farko. Dalili kuwa shi ne, yanayin tattalin arziki na iyayena ba ya da kyau tun ina yarantaka. Tun daga wancan lokaci dai, na dau aniyar tallafa wa sauran kananan yara idan na samu kudi'.
Bayan da Madam Meng Xiaoyan ta sauke karatu a Jami'ar Beijing a shekarar 1999, sai ta je wata makarantar sakandare ta gundumar Xin ta lardin Henan bisa son ranta domin yin aikin koyarwa na tsawon shekara guda. Wannan dai ya kasance sabon masomi ne na yin hidimomi da take yi. A kauyukan lardin Henan, Madam Meng Xiaoyan ta gano cewa, babbar matsala dake gaban wasu kananan yara ita ce suna gazawa wajen yin kirkire-kirkire. A cikin wannan shekara guda, Madam Meng Xiaoyan ta bi hanyoyi da dama don kara kwarin gwiwar wadannan kananan yara. Kamar yadda Hausawa sukan fadi cewa " Kwalliya ta biya kudin sabulu". Bayan 'yan shekaru kawai, wasu 'yan makarantarta sun samu shiga Jami'o'I da kolejojin birnin Beijing. Da Madam Meng Xiaoyan ta tabo kan lamarin, sai ta yi murmushi da fadin cewa: ' Lallai abin farin ciki ne a gare mu masu aikin sa kai domin mun samu damar tallafa wa kananan yara na wadannan wurare dake fama da talauci da kuma karfafa aniyarsu'.
Bayan da Madam Meng Xiaoyan ta dawo nan Beijing daga Henan, ta soma yin aikin bada agaji a fannin shari'a. Ta fadi cewa, lokacin da take yin aikin koyarwa a lardin Henan, ta gane daraja da kuma ma'anar ayyukan sa kai da take yi. Hakan ya kara kwarin gwiwarta wajen rokon zama mai aikin sa kai domin taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008.
Madam Meng Xiaoyan tana cike da kyakkyawar fata ga taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. A matsayin daya daga cikin wadanda suka yi rajistan zama masu aikin sa kai na taron wasannin Olympics, yanzu Madam Meng Xiaoyan tana jiran amsa daga kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing. Ta kuma bayyana ra'ayinta cewa, idan kowa ya bada ilmin sana'a da ya samu da kuma nuna kwarewarsa wajen aiki, to tiamako ne yake bai wa taron wasannin Olympics.
Jama'a masu saurare, shekara guda ke nan da ta rage ga gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Yanzu ana gaggauta share fagen taron wasannin Olympic na Beijing da kuma taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Ana bukatar samun masu aikin sa kai da yawansu ya zarce dubu dari biyar domin wadannan tarurruka. Madam Meng Xiaoyan ta ci gaba da cewa : ' Ya kamata kowa da kowa ya nuna himma da kwazo wajen yin abubuwa ko da kanana. Wane irin tasiri ne taron wasannin Olympic zai kawo wa birnin Beijing ? A ganina, ba wai dama iri daban-daban na kasuwanci ba. A'a, za a iya kyautata halayyar mazauna birnin Beijing ta hanyar gudanar da wannan gagarumin taron wasannin Olympics.' ( Sani Wang )
|