Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-02 15:36:54    
Gada mafi girma da ta ratsa teku a duniya

cri
A wannan mako, za mu amsa tambayar malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin garin Keffi da ke jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, wanda ke sauraronmu a kullum. Malam Sanusi ya turo mana wasika a kwanan baya da ke cewa, a kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata sabuwar gada da za ta ratsa teku daga birnin Shanghai zuwa birnin Ningbo da ke cikin lardin Zhejiang, kamar yadda ya ji wannan labarin, gadar za ta zama ita ce mafi girma a duniya kuma tsawonta zai kai kilomita 36. Tambayarsa ita ce shin a halin yanzu, kamar kilomita nawa ne daga Shanghai zuwa Ningbo?

A ranar 26 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki, an kaddamar da wata gada mai tsawon kilomita 36 wadda ta ratsa bakin teku na Hangzhou, wadda har ma ta kasance gada mafi girma da ta ratsa teku a duniyar yau, ana kuma sa ran za a fara aiki da gadar kafin taron wasannin Olympics da za a shirya a shekara mai zuwa, kuma a lokacin, gadar za ta kyautata halin da ake ciki a fannin sufuri a tsakanin biranen Shanghai da Hangzhou da Ningbo.

An dai fara gina wannan gadar a ran 14 ga watan Nuwamba na shekarar 2003, kuma bisa shiri, za a shafe tsawon shekaru biyar ana gina ta. Gadar tana da manyan hanyoyin mota guda shida, a karkashin gadar kuma, akwai ginshikai biyu, wadanda za su taimakawa jiragen ruwa iya tafiya cikin sauki. Don fuskantar matsalar zaizaya da ruwan teku zai iya kawo wa gadar, an kuma dauki fasahohin zamani na hana zaizayewa wajen gina gadar.

A hakika, ba a rasa samun irin wadannan gadojin da suka ratsa teku ba a duniyarmu, amma idan an kwatanta su da gadar nan da muka yi muku bayani, za a gane cewa, wannan gadar da ta ratsa bakin teku na Hangzhou ta sha banban. Na farko dai, an tsara wannan gada don amfanin shekaru 100 na rayuwa, wato za a yi tsawon shekaru 100 ana amfani da ita, wadda ko a Amurka ko a Ingila, ba safai a kan gano irinta ba. Sa'an nan, gadar tana da manyan hanyoyin mota shida, wadanda motoci ke iya tafiya da saurin kilomita 100 a cikin kowace awa a kansu, wannan shi ma abin da ba safai a kan gani ba ne. Sai kuma a wajen kulawa da gadar, tun lokacin da aka fara gina gadar har zuwa lokacin da ake aiki da ita a cikin tsawon shekaru 100, ana amfani da fasahohin zamani wajen sa ido a kan ingancin gadar da kuma ba da agaji.

To, malam Sanusi, a cikin tambayarka, ka ce, gadar ta ratsa teku daga birnin Shanghai zuwa birnin Ningbo, to, bari in yi maka dan gyara, a hakika dai, gadar ta tashi ne daga birnin Jiaxing a arewa, sa'an nan, ta ratsa teku a bakin Hangzhou, kuma daga karshe dai, ta kammala a birnin Ningbo. Wato ta hada birnin Jiaxing da birnin Ningbo ke nan, a maimakon birnin Shanghai da birnin Ningbo. Ko da yake gadar ba ta hada birnin Ningbo da Shanghai kai tsaye ba, amma bayan da aka kammala gadar, za a iya rage nisan hanyar zuwa birnin Ningbo daga birnin Shanghai da kilomita fiye da 120. Wannan zai taimaka wajen kyautata halin da ake ciki a fannin sufuri a shiyyar, haka kuma zai taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar.(Lubabatu)