Ran 1 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya ba da wani bayani cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen duniya domin kyautata tsarin gurguzu da kanta da kuma bunkasa shi, a maimakon neman canza halin tsarin gurguzu na kasar Sin.
Rahoton da aka gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya ambata cewa, kasar Sin tana gudanar da babban sha'anin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen duniya bisa kyawawan fasahohi masu daraja da shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na zuriya ta farko da aka mayar da Mao Zedong tamkar kwayarsu suka samu daga wajen samar da tunanin Mao Zedong, haka kuma da jagorancin jam'iyyar da jama'ar dukkan kabilun kasar domin kafa sabuwar kasar Sin da samun nasarar yin juyin juya hali na gurguzu da yin ayyukan gurguzu, da kuma neman samun ka'idojin ayyukan gurguzu. A lokacin da yake yin bayani kan hakan, kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya yi hasashen cewa, irin wannan shawarar da aka yanka ta dace da abubuwan gaskiya da suka faru a tarihin kasar Sin, haka kuma, zai iya cin jarrabawar da aka yi ta fuskar tarihi da jama'a da kuma abubuwan gaskiya.(Tasallah)
|