Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-01 16:08:30    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (6)

cri

---Mai kishin tattara samfurorin mallaman bude littafi.Da akwai wani dan makarantar middle wanda ya ke da shekaru 17 da haihuwa,yana sha'awar tattara samfurorin mallaman bude littafi.shi ya sa mutane da yawa suna kiransa malamin mai kishin malamin bude littafi.Sunansa Zhang Ran yana zama a gundumar Yanshou na lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin.nau'o'in malaman bude littafin da ya tattara sun wuce dari shida,daga cikinsu talatin da ba a taba ganinsu ba.

---Direban motar taxi ya mayar da kudin da aka bace a motarsa.Wani direba mai fadin gaskiya a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin ya mayar da kudin Sin RMB yuan dubu 185 da fasinjoji guda biyu suka bace a cikin motarsa tare da taimakon gidan rediyo mai kula da zirga zirgan motocin gari a ranar lahadi da ta shige.An gano wadannan kudade ne a cikin wata jakar roba a kujerar bayan dake cikin mota.Da direba,Mr Liu ya gano kudin sai ya buga waya zuwa ga gidan rediyo mai kula da harkokin zirga zirga da ya watsa labarin cigiyar mai bace kudin.fasinjojin nan biyu miji da matarsa ne da suka samu labarin,sai sun bugo waya ga kamfanin da wannan direban ke ciki,sun je wurin kamfanin sun samo kudin da suka bace.

---Mazaunan birnin An'shan suna mamaki kan bullowar dodon kodi.Bayan da aka yi ruwan sama,mazaunn birnin An'shan sun gano dodon kodi dubu dubai a wuraren da suke zaune,wasu ma sun hau itatuwa,mazaunan ba su san inda suka fito ba.Wasu masana ilimin namun daji sun yi bincike daga baya sun ce dodon kodi sun fito daga wani kwalbati na dab da wata masana'anta.dalili kuwa shi ne ruwan sama ya cika kwalbati shi ya sa dodon kodi suna neman samun sabbin wuraren zama,sun fito har ma wasu sun hau itace.Wani mazauni ya ce "ban taba ganin yawan dodon kodi kamar haka ba a rayuwata."

---Wani malamin mai da misalin koyo na makarantar firamare.Wani malamin koyarwa a makarantar firamre na gundumar Wuning na lardin Jiangxi da aka kiransa Mr Xiong Yihua,ba ma kawi ya yi aikin koyarwa a makarantar ba har ma ya tuki jirgin ruwan da ya dauke almajiransa cikin shekaru 33 da suka gabata.shi ya sa aka mai da shi misalin koyo ga sauran malaman kasa.Mr Xiong ya kuma sha wahala sosai sabo da ya ke zaune cikin duwatsu,ya kan kashe mintocin arba'in wajen zuwa makarantar da ya ke aiki.Duk da haka shi bai gaji da aikinsa ba,ya ce idan almajiransa suna bukatarsa zai ci gaba da haka.

---Mai laifi ya tuba.Da akwai wani mutum mai baskur a gundumar Xinfeng na lardin Jiangxi na kasar Sin.ya kan tuki baskursa da saurin gaske ba tare da kula da sauran matafiya ba.A farkon wannan wata ya yi gudu mai saurin gaske da baskurinsa har ya kada wani mutum a kan hanyar mota.mutum da ya kada a kwance a hanya,shi matuki bai kula da shi ba har ma ya tafi abinsa.Da 'yan sanda sun isa,sun kai mutumin da ya kada cikin asibitin.bayan da aka yi bincike an kuma kama mai baskurin.Aka kawo shi a asibitin,ashe mutumin da ya kada,dangin iyalinsa ne,sai ya tuba.

---ko tsuntsaye ma suna son yanci.ma'aikatan gidan dabobi na birnin Xiamen na lardin Fujian suna neman tsuntsaye biyu namiji da mace masu kyaun gani da ake kira "peacock" da suka tsira daga gandun tsire tsire na Wanshi a karshen makon jiya.Daga baya an same su a kan wani tudu na kusa da jami'ar Xiamen a ranar lahadi.Ma'aikata daga hukumar kula da gandun daji ta wurin suna so su kama tsuntsaye suka yi musu kawanya,duk da haka sun yi iyakacin kokarin neman tsira ta hanyoyi daban daban.

---Mutane biyu suna neman satar injin bulldozer.'Yan sanda sun tsare mutanen biyu da aka yi tuhumarsu da satar injin bulldozer cikin yin amfani da wani babban injin daga kaya da mota a gundumar Feixi na lardin Anhui na kasar Sin.

A makon jiya a wani kauye da akwai mutum da ake kiransa Yu.Ya farka sabo da karar injin ya dame sa,ya ga mutane biyu da suka yi amfani da injin mai daga kaya da babbar mota suna daga injin bulldozer.Da ya san wannan injin bulldozer na makwabcinsa wanda ba ya gida kwanan baya.Sai nan da nan ya sanar da 'yan sanda da wayar salula.Ba tare da bata lokaci 'yan sanda sun isa wurin sun kama wadannan mutanen biyu.

---Wani mutum ya ja mota da hancinsa.A karshen makon jiya a birnin Haikou dake kudancin kasar Sin,wani mutum ya ja mota da hancinsa har motar ta yi tafiya mai nisa mita goma.Mutumin nan sunansa Wang Chuntai yana da shekaru 40 da haihuwa.ya sa kugiyar karfe biyu a hancinsa ya nannade su da igiya,ya hada igiya da mota,sa'an nan ya ja.Ya samu nasara.Mr Wang ya ce ya yi haka ne cikin shekaru da yawa.ya yi shirin gwada su a manyan birane na kasar Sin.(Ali)