Ran 25 ga watan Oktoba, a nan Beijing, an rufe cikakken taro na karo na 9 da kwamitin kula da harkokin taron wasannin Olympic na Beijing na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa wato IOC ya shirya. Bayan taron, shugaba Hein Verbruggen na kwamitin kula da harkokin taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya sami kyakkyawar nasara. An bude wannan cikakken taro ne a ran 23 ga watan Oktoba, inda kwamitin kula da harkokin taron wasannin Olympic na Beijing da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing suka yi mu'amala da tattaunawa kan ayyukan gina filaye da dakunan wasa da sayar da tikitoci da bai wa 'yan wasa hidima da dai sauransu.
Tun daga ran 30 ga watan Oktoba da karfe 9 da safe, aka kaddama da aikin sayar da tikitocin kallon gasannin taron wasannin Olympic na Beijing a mataki na 2 a hukunce, za a sayar da tikitoci miliyan 1 da dubu 850 a wannan mataki. An labarta cewa, ana bin manufar 'na farkon zuwa, na farkon saya' a wannan mataki, haka kuma, in tikitocin sun kare, to, za a sa aya ga aiki na wannan mataki, ta haka, karin mutane za su cimma burinsu na wasan Olympic.
Ran 24 ga wata, a birnin Wuhan da ke tsakiyar kasar Sin, an bude bikin nune-nune mai lakabi haka 'tarihi da makoma game da yaki da amfani da magani mai sa kuzari har na tsawon shakaru 40 a cikin wasannin Olympic'. An ce, an kiyasta cewa, za a yi bincike kan mutane misalin 4500 a fannin yin amfani da magani mai sa kuzari a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, yawansu ya karu da rubu'i bisa na taron wasannin Olympic na Athens a shekarar 2004.
Ran 27 ga watan Oktoba, a nan Beijing, an rufe babban taron wasannin motsa jiki da muhalli na duniya a karo na 7, inda aka zartas da 'sanarwar Beijing game da wasannin motsa jiki da muhalli'. Sanarwar ta nuna amincewa sosai kan ayyukan kiyaye muhalli da ake yi domin taron wasannin Olympic na Beijing. Ban da wannan kuma, sanarwar ta nuna cewa, shirya taron wasannin Olympic na Beijing na gaggauta kyautata muhallin duk birnin Beijing. Yanzu Beijing na inganta yin amfani da makamashi yadda ya kamata, da yin amfani da makamashin da aka iya sake amfani da shi, da daukar matakai da ayyukan zirga-zirga na kiyaye muhalli, da kuma rubanya kokarin dasa bishiyoyi da ciyayi a birnin, ta haka, Beijing ta yi iyakacin kokarinta wajen rage da kuma kawar da iska mai dumama yanayi da ake fitarwa, haka kuma, an iya nuna babban yabo kan wadannan manufofi da ayyuka.
A matsayin taron wasannin motsa jiki na duk kasa a karo na karshe da kasar Sin ta kira kafin taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, a ran 25 ga watan Oktoba, a birnin Wuhan na kasar Sin, an bude taron wasannin motsa jiki na biranen kasar Sin a karo na 6. Za a rufe taron a ran 3 ga watan Nuwamba.(Tasallah)
|