Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:46:54    
Dakin tseren kekuna na Laoshan

cri

A yammacin birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda za a yi taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa, akwai wani dakin tseren kekuna mai suna Laoshan, inda 'yan wasan tseren kekuna za su yi karawa da juna domin samun lambar zinariya a cikin kananan gasannin tseren kekuna guda 12 a shekarar gobe.

Fadin dakin tseren kekuna na Laoshan ya kai kadada misalin 6.6. Tsawon hanyoyin tseren kekuna ya kai mita 200. 'Yan kallo dubu 6 suna iya kallon gasa tare a cikin wannan dakin wasa. Abu mafi jawo hankulan mutane a fannin zayyanar wannan dakin wasa shi ne siffarsa ta yi kama da wata tasa. Masu zayyanar dakin wasan sun zayyana wannan dakin tseren kekuna bisa tsarin yanayin kasa na wurin da aka gina shi yadda ya kamata, ta haka muhimmin bangaren dakin wasan mai siffar tasa ya yi kama da wata hular kwano da 'yan wasan tseren kekuna kan sa a kawunansu a cikin gasa. Duk dakin tseren kekuna na Laoshan ya nuna sigar musamman ta wasan tseren kekuna, wato 'yan wasan tseren kekuna na rubanya kokarinsu domin kara samun sauri a duk ransu.


1 2